‘Yan bindiga sun addabi dubban manoma a jihar Taraba, inda hakan ya hana su zuwa gonakinsu domin yin noma, hakan ya kuma hana kusan al’ummomi 20 da ke yin noma a yankuna daban-daban yin noma.
An ruwaito cewa, ‘yan bidigar sun hakan manoman zuwa gonakinsu kamar wadanda ke yankin Gassol da ke a cikin karamar hukumar Bali, inda suka yi barazanar kashe duk manomin da suka samu ya je gona domin yin noma.
Lamarin sai kara munana yake yi a yankunan a kullum, inda kuma aka ruwaito cewa, ‘yan bindigar sun sace wasu manoman da kuma masu kiwon shanu, inda lamarin ya tilasta su yin hijira zuwa Jalingo, Tella da Mutumbiyu.
An ruwaito cewa, a cikin makwannon da suka gabata, ‘yan bindigar sun yi garkuwa da sama da manoma 50, inda kuma suka bukaci a basu kudin fansa daga naira miliyan 5 zuwa naira miliyan 7 a kan ko wanne manomi daya, kafin su sako su.
Akasarin wadanda lamarin ya rutsa da su, ya tilasta masu sayar da kadarorin su domin su biya ‘yan bindigar kudaden fansa.
Wani bincike ya nuna cewa, ‘yan bindir na dorawa wasu manoman haraji kafin su bar su suje gonakan su domin noma su.
‘Yan bindigar wadanda ke zuwa a kan baburansu, sun kuma tarwatsa mazauna yankunan Jauro Manu da BabaJoli da Garin da Gidado da Anema da kuma wadanda ke da zama a kauyukan da ke karamar Bali.
Sauran al’umomin da ke ci gaba da fuskantar barazanar ta ‘yan bindiga a jihar sun hada da, Baba Also da Adamu Ja da Garin Simaila da Nabayi da garin Karfe da Yola Karejo da Garin Gaga, Yarima da TibKwayo da Kumburo da Wayo Kwayosa da Gidan Iro da kuma Gidan Jafala.
Tuni dai, manoman da ke wadannan yankunan suka kaurace wa gonakansu da kuma amfanin gona da suka shuka.
Daya daga cikin manoman wanda bai bukaci a ambaci sunansa wanda kuma shi ma, ‘yan bindigar suka taba sace wa, ya bayyana cewa, sau uku ana yin garkuwa da shi, inda sai da ya biya kudin fansa naira miliyan 5.4 kafin a sako shi.
An ruwaito cewa, hatta masu rike da mukaman gargajiya wasu yankunan jihar sum aba su tsira daga sacewar da ‘ yan bindigar ke yi masu ba, inda har ta kai ga, sun sace Dagatan kauyukan Maigemu, Maisamari da kuma na Garing Barau suka kuma kashe su.
Sun kuma sace Dagacin kauyen Gunduma, Mallam Wali Gunduma, amma daga baya suka sako shi bayan an biysa su kudin fansa.
‘Yan bindigar sun kuma hana manoman da ke a yankunan zuwa noma gonakansu a kakar noman bana.
An ruwaito cewa, sama da kashi 70 na jimlar Shinkafar da Masara da Gyada da sauran amfanin gona, da ke noma da kuma m wa jihar Taraba na fitowa ne daga Bali da kuma Gassol.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa, “ Muna noma manyan amfanin gona da suka hada da, Shinkafa ‘yar gida, Gyada da sauran amfanin gona, amma a yanzu, ‘yan bindigar sun karbe akasarin gonakan da ake noma wa a yankunan , inda ya kara da cewa, hakan ya janyo aikin noma ya ragu matuka a yankunan jihar”.
Wani mai sana’ar sayar da Shanu a jihar Alhaji Boshe ya sanar da cewa, sau hudu masu garkuwar suna sace shi kuma a duk lokacin da suka sace shi, sai ya biya kimanin naira miliyan 5 kudin fansa kafin su sako shi.
Alhaji Boshe ya kara da cewa, lokacin da suka sace shi a watan da ya gabata, sai da ‘yan uwansa suka ranto naira miliyan 5.5 kudin fansa tare da biyan kudin ruwa domin a sako shi.
A cewar Boshe, akasarin Fulani Makiyaya a wasu yankunan da ke a jihar, suka sayar da kimain shanu 300 saboda biyan kudin fansa ga ‘yan bindigar kafin su sako su.
Ya kara da cewa, saboda barazanar masu garkuwar, Fulani Makiyya da dama sun ta shi daga matsugunan su, inda ya bayyana cewa, idan har mutum babban manomi ne ko babban mai kiwo a yankunan za ka ci gaba da fuskantar barazanar ta ‘yan bindigar domin ako wanne lokaci, masu kai wa ‘yan bindigar bayanan sirri suna bibiyar manoman da Fulani Makiyyan, musamman idan sun yi wata hada-hadar cinikayya.