Daga Rabiu Ali Indabawa,
Rahotanni daga Jihar Borno na nuni cewa alal a kalla, dakarun Sojojin Nijeriya bakwai suka rasa rayukansua sanadin wani mumunan harin kwantan baunan da ‘yan ta’addar Boko Haram suka kai musu a Jihar Borno. Sojojin da wannan hari ya shafa su ne runduna ta 153 Task Force Battalion dake Karamar Hukumar Marte, a Borno.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce, ‘yan ta’addar sun kai wa sojin harin kwantan baunan ne misalin karfe 10 na safiyar ranar Talata. Sojojin sun yi ta maza inda suka yi kokarin dakile harin da fitittikar ‘yan ta’addar. Amma duk da jaruntar da suka nuna, ‘yan ta’addar sun galabaita sojojin “saboda ba su iya jure ruwan wutar da ‘yan ta’addar ke yi masu ba,” cewar majiyar.
Majiyar ta ce yanzu an mayar da sauran Sojojin dake Marta Karamar Hukumar Dikwa. Kawo yanzu, hukumomi sun ankarar da rundunar Sector 3, musamman wadanda ke Baga, Cross Kauwa, Kekeno da Monguno da su kasance cikin shiri. Majiyoyi a gidan soja na nuna cewa harin wannan ranar shi ne karo na uku da ‘yan ta’addan su ka kai cikin wata guda.