‘Yan bindiga da ake kyautata zaton mambobin kungiyar Boko Haram ne sun kai hari kauyen Lawan Mainari da ke kusa da hanyar Mainok da ke tsakanin titin Damaturu zuwa Maiduguri a jihar Borno tare da yin garkuwa da matafiya da daman gaske.
Ganau sun shaida cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen da ke da tazarar kilomita 40 da cikin birnin Maiduguri babban birnin jihar Borno.
An nakalto cewa ‘yan bindigan sun yi garkuwa da matafiya masu yawa tare da banka wa motoci 9 da tiraktocin da suka dauko kayan abinci wuta.
Har zuwa yanzu dai hukumomi ba su ce komai ba inda matafiya da dama cikin firciki suka tsaya a kauyukan da ke kusa da inda lamarin ya faru domin kare lafiyarsu yayin da wasu kuma suka juya zuwa cikin Damaturu da ke jihar Yobe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp