Hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutum hudu a wani rikicin da ya barke tsakanin Hausawa mazauna Lafiya da ‘yan kabikar Lunguda a garin Lafiya cikin karamar hukumar Lamurde ta jihar Adamawa.
Mazauna garin sun tabbatar da cewa rikicin ya barke ne akan gonaki, inda suka bayyana cewa mutane da dama sun mutu sakamakon barkewar rikicin.
- 2023: Gwamnonin APC Daga Arewa Sun Kafe Kai Da Fata Sai Dan Kudu Ya Yi Takara
- Adamu Ya Kori ‘Yan Jarida Daga Ofishin APC Bayan Tutsun Da ‘Yan Jam’iyyar Suka Tayar
Maista Bulus Daniel, shi ne shugaban karamar hukumar Lamurde, ya tabbatar da mutuwar mutum biyar biyo bayan tashin rikicin da safiyar ranar Litinin.
Wani mazaunin yankin ya ce “Ni bana garin amma ina hanyar dawo wa, duk wani labarin da yake fitowa daga yankin ka dauke shi tamkar karya, jami’an tsaro basu bada cikakken rahoto ba tukuna.
“Abinda zan iya shaida maka shi ne kusan mutum 4 ne suka rasa rayukansu, amma a hukumance bamu kai ga kididdige adadin mutanen da lamarin ya shafa ba” inji Bulus.
Wani ganau, da ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaidawa LEADERSHIP Hausa cewa “kwanakin baya mutanenmu su nje gona, sai aka sassari wasu mutane mu kuma muka sanarwa jami’an tsaro da shugaban karamar hukuma.
“Ya bamu hakuri kada mu dauki wani mataki, to yau wasu sun fita gona sai mutanen Lunguda suka kashe mana wani mutum mai suna Sani, shi ne ya kawo rincabewar rikicin, yanzu an kashe mana mutum biyu, muna da labarin akwai wasu biyu ko uku da aka kashe a wajan gari.
“Mun kai kuka gun hukumomi amma har yanzu ba su iya daukar matakin shawo kan matsalar ba, kuma kullum mutanenmu ake kashewa” inji Mazauna yankin.
Itama rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da rikicin, sai dai tace kura ta lafa.
DSP Suleiman Ngoroji, shi ne jami’in hulda da jama’a na rundunar, ya ce “an jibgi runduna ta musamman a yankin domin dakile rikicin.