Abdulazeez Kabir Muhammad" />

‘Yan Fashi Sun Kashe Ma’aikacin Gwamnati A Osun

Wasu gungun ‘yan fashi sun harbe wani ma’aikacin gwamnati har lahira mai suna Mista Adenipekun Ademiju yayin da suke gudanar da fashi akan babban tirin Ife zuwa Ibadan, dake jihar Osun. Ademiju, wanda aka fi sani da Okere, ma’aikacin karamar hukumar Atakumosa ta yamma ya dauki shatar motar haya a Osu a kan hanyar sa ta zuwa Ibadan kafin lamarin ya auku a Ikire.

Rahotanni sun bayyana cewa an harbi Ademuji lokacin da yan fashin ke harbi ta koina don tilasta wa motocin dake tunkarar su tsayawa. Wani wanda lamarin ya auku a kan idon shi ya sanar da cewa, ‘yan fashin sun kashe mutumin ne bayan sun yi yunkurin harbi direban motar amma basu same shi ba sai suka samu wannan mutumin.

‘Yan fashin sun ajiye gawar mamacin akan babban titin yayin da suka tafi da motar shi. Jami’in hulda da jama’a na yan sandan jihar, Folashade Orodo ya tabbatar wa manema labarai cewa har yanzu suna gudanar da bincike akan lamarin.

Exit mobile version