Yan Jam’iyar APC A Zamfara Sun Gudanar Da Zanga-Zanga A kan A Cire Shugaban Jam’iyar Na Kasa

‘Yan jam’iyar APC a jihar Zamfara suna sun gudanar da gagarumar zanga-zanga a kan kin amince wa da Shugabancin Shugaban na kasa Adams OShimole, sakamakon kin amsar zaben fid da gwani da Shugabanin jam’iyar na jiha da suka yi.sun gudanar da zanga-zangar ne a Gusau babban birnin jihar Zamfara.
Shugaban kungiyar Shugabanin kananan hukumomin na jam’iyar ne,Alhaji Aminumu Abdullahi Gama giwa , ya gatar da jawabi kamar haka,ya bayyana cewa’ Shugaban jam’iyar na kasa watau Adam Oshimole bai cancanji da Shugabancin jam’iyar ba na kasa dan yana wariyar launin fata,kuma.yana hana wasu jahohin rawar gaban hanci,kuma bai nemar wa Shugaban kasa jam’a sai ma naima. Korar su ya ke.
Kuma mu Zamfarawa baya kaunar mu bamuga dalilin kin amsar zaben mu da na fidda gwani da mu kayi.
Dan haka mu ke kira ga sauran ‘yan jam’iyar APC na kasa da su maramana baya wajan kauda wannan baisan ciyasa ba kuma.ba dan siyasa ba ne sai naiman dakushe mana siyarmu ya ke
Dan haka muke kira da kakkausar murya da Shugaban kasa da ya sa a sauke Adam Ashimole dan samun nasara a zabe mai zuwa.
Kuma.anan take ya mika sakataren jam’iyar na jihar Zamfara, Hon Sani Musa Molo ,Takardar kokensa ‘yan jam’iyar APC na kananan hukumomi sha hudu da ke jihar Zamfara bamu gamsu da jagorancin sa dan haka a gaggauta canzamana shi.
Sakataren Hon Sani Musa Molo ya amshi takarkar kuken nasu kuma ya dau alwashin mikata ga Datawan Shugabanin na kasa dan sharema su hawayen su.akan kin aminta da Shugabancin Shugaban na kasa Adam Oshimole.
Wanda ya wakilci Shugaban kananan hukumomi a wajan taron ,Ho Salisu Isa Dan Gulbi Shugaban Karamar Hukumar Maru,ya bayyana godiyar sa ga ‘yan jam’iyar APC da suka.halarci wannan zanga zangar kuma akayita cikin limana da kwanciyar hankali.kuma muna fatan Datawan jam’iyar APC na kasa zasu duba koken mu dan daukar matakin gagawa akan mai naiman naksa jam’iyar APC a jihar Zamfara

Exit mobile version