Hussaini Yero" />

‘Yan Jamiyyar APC Dubu Biyar Ne Suka Koma PDP A Gusau 

‘Yan jamiyyar adawa ta APC dubu biyar ne suka canza sheka zuwa jamiyyar PDP mai milkin jihar a karamar hukumar mulki ta Gusau babban birnin Jihar Zamfara.

Shugaban jamiyyar PDP na karamar hukumar Gusau, Alhaji Tukur Dan Fulani ne ya bayyana haka a lokacin bikin amsar masu canjin shekar a filin tsohuwar Tasha da ke Gusau.

‘ Alhaji Tukur Dan Fulani, ya bayyana wasu daga cikin dalilan da yasanya wadannan kungiyoyi takwas da ke dauke da mutane dubu biyar suka ga ya zama dole su mara wa Gwamna Bello Matawallen Maradun, baya da kuma zamowa cikin jam’iyyar PDP.saboda samun nasarar tsaro da aka samu.

Shugaban ya bayyana dalilan kamar haka, samun nasararkyautatuwar tsaro wanda a baya al’ummar jihar Zamfara na cikin tsaka mai wuya dangane da matsalar tsaro,Noma ya gagara, ‘yan Kasuwa basa iya Shiga kasuwannin  kauyuka, sabo da gamuwa da fushin ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane da satar Shanu da kisan gilla da suke wa al’umma a wancan lokacin, inji shugaban.

Tukur Dan Fulani, ya kara da cewa, ‘ganin yadda cikin shekara guda da mulkin Gwamna Bello Matawallen Maradun, na samun nasara magance matsar mahara da masu garkuwa da mutane da ‘yan ta’adda suka ga lallai ya zama wajibi su marawa gwamnatin PDP karkashin jagorancin Gwamna Matawallen Maradun baya don ganin kudirinsa ya cika na samar da tsaro a fadin jihar.

‘ Kuma ayyukan da mai girma Gwamna Matawallen Maradun keyi a fadin jihar na cigaban al’umma suma na daya daga cikin dalilan da ya sanya ‘yan adawa masu sonci gaban jihar Zamfara dawowa cikin jamiyyar PDP a Gusau.

Daya daga cikin shugabannin kungiyoyin da suka komo jam’iyyar ta PDP,Ibrahim Asharuwa daga Mayana, ya bayyana cewa, Su ba zasuyi ma Allah butulciba akan cigaban da aka samu a fannin tsaro da ayyukan cigaban al’umma da tallafamasu, a karkashin jagorancin gwamnatin Gwamna Bello Matawallen Maradun.

Don haka,“Mukaga ya zama wajibi mu maramasa baya mu aje adawa tun da ya tafiyar da gwamnatinsa tsakani da Allah, in ji Ibrahim Mayana.

Kantoman karamar hukumar Gusau, Honorabul Sunusi Muhammad Sarki, ya bayyan jin dadinsa da godiya ga Allah akan samun nasara a kan ‘yan adawa da suka gamsu da ayyukan Gwamna Matawallen Maradun kuma ya sanya suka dawo cikinmu.

Honorabul Sarki, ya dau alwashin tafiya da sabbin ‘yan jam’iyyar ba tare da nuna masu bambanci ba. Yanzun sun zama daya da mu, kuma da yardar Allah zamu cigaba da yin ayyukan ci gaban al’umma a fadin karamar hukumar mu ta Gusau.

Daraktan kamfen na Gwamna Bello Matawallen Maradun,Honorabul Jamilu Zannan Gusau, ya bayyana cewa, ya kamata Shugabannin jam’iyyar PDP na kananan hukumomi suyi koyi da takwarorinsu na karamar hukumar Gusau, a wajen  jawo ‘yan adawa zuwa jam’iyyar PDP a kananan hukumominsu.

Zannan Gusau, ya kara da cewa, taron jam’iyyar PDP taro ne na arziki kuma yana taimakawa wajen farfado da tattalin arziki, don a yau hatta masu sayar da ruwan sha a Gusau, sun samu alheri da kananan ‘yan kasuwa don haka taron mu taron arziki ne wanda al’umma ke amfana dashi.

A nasa jawabin, babban bako mai jawabi, Mataimakin Gwamna, Honorabul Mahadi Aliyu Gusau,da ya samu wakilcin, Kwamishinan Ilimi, Ibrahim Abdullahi Spirow,ya bayyana cewa,“Wadannan mutanen da suka dawo jam’iyyar PDP ya tabbatar mana da cewa, su cigaban jihar Zamfara suke so ba mahasada bane.

Don haka, muke kira ga ‘yan adawa da su hakura da hukuncin Allah su zo mu tafi tare don ganin ci gaban jihar ta Zamfara, mu kofar mu a bude take wajen tafiya da kowa da kowa.

Kuma muna tabbatar ma wadanda suka shigo wannan jam’iyyar ta PDP za mu tafi tare da su kafada da kafada don cigaban jihar,in ji wakilin mataimakin Gwamnan.

Exit mobile version