Khalid Idris Doya" />

‘Yan jarida Da ‘Yan Sanda Sun Sabunta Kyakkyawar Dangantakarsu A Bauchi 

Kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Bauchi (NUJ) ta shirya zaman tattaunawa a tsakanin ‘yan sanda da kuma masu farauto labarai daga gidajen jaridu daban-daban domin daddalewa tare da sahale muhimman batutuwan da suka shafi kyautata dangantaka a bangaren aiyukansu.

Ganawar wacce ta gudana a shekaran jiya a cibiyar NUJ da ke jihar, an shirya ganawar ce da zimmar shawo kan wasu ‘yan baturuwan da suka shafi rashin fahimta a wasu fannonin a tsakanin ‘yan sanda da kuma wakilai kafafen sadarwa daban-daban da zimmar dinke gibin da ke akwai don tabbatar da aikin sadarwa na tafiya yadda ake so bisa gudanar da aiyukan kan dokoki da ka’idoji.

Shugaban kungiyar’yan jarida na jihar Malam Umar Saidu shine ya jagoranci zaman tare da tabbatar da an samu kyakkyawar fahimta a bangaren aiki.

A jawabin bayan taron da aka fitar, an cimma matsayar cewa akwai gayar bukatar samar da kyakkyawar alaka a tsakanin ‘yan sanda da kuma su kansu ‘yan jarida domin tabbatar da yin aiki mai nagarta.

Har-wa-yau an kuma nemi ‘yan jarida musamman wadanda suke farauto labaran da suka shafi harkar tsaro da su kasance a kowani lokaci masu gudanar da aiyukan su da kwarewa a duk lokacin da suke neman bayani daga wajen ‘yan sanda dangane da wasu baturuwan da suka shafi tsaro.

Ganawar ta kuma cimma matsayar cewa ‘yan sanda za su ke tabbatar da baiwa ‘yan jarida muhimman bayanai a kan lokaci tare kuma da shawartar ‘yan jarida da suke bin dokoki da ka’idoji wajen neman labaran da suka shafi tsaro musamman na bincike da bin kwakwaf domin tabbatar da baiwa jama’a sahihi kuma ingattatun labarai.

‘Yan sanda wadanda suka samu wakilcin jami’in da ke magana da yawunsu PPRO, DSP Ahmed Wakili an bukace su da su rungumi yin aiki tare da ‘yan jarida domin kyautata aiki a kowani lokaci da baiwa kowani bangaren cikakken damar gudanar da aikinsa yadda doka ta ba shi dama.

An kuma yaba wa NUJ a bisa shirya irin wannan taron, inda aka ce wannan shine karo na farko da aka samu irin wannan zaman a tsakanin ‘yan Sanda da ‘yan jarida a jihar.

NUJ reshen jihar ta yi alkawarin cewa za a ke gudanar da irin wannan zaman duk bayan wata uku domin zaunawa wuri guda tare da baje kolin korafe-korafe da baturuwa domin ganin an magance cikin laluma da salama.

A yayin taron wakilinmu ya labarto cewa ‘yan jarida sun baiwa jami’an watsa labaran ‘yan sandan shawarorin yanda zai kyautata aikinsa tare da samun nasarar kammalawa lafiya, inda shi ma ya baiwa ‘yan Jaridun irin wannan shawarwarin domin su ke samun bayanai daga garesu ba tare da shan wuya ba.

 

Exit mobile version