Connect with us

LABARAI

’Yan Kanywood Sun Fara Karrama Malamai

Published

on

kungiyar masu shirya finafinan Hausa ta Kanywood (MOPPAN), reshen Jihar Filato, ta karramar fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ke zaune a garin Jos, kuma Daraktan Ilmi na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa reshen Jihar Filato, Ustaz Abubakar Imam Bala Gana kan gudunmawar da ya ke bayarwa wajen zaman lafiya ta hanyar wa’azuzzukan da ya ke gabatarwa a gidajen rediyo da talabijin na jihar ta Filato.
kungiyar ta karramar malamin ne a karshen makon da ya gabata a garin Jos.
Da ya ke jawabi a wajen taron, Sakataren kungiyar Attahiru Babayo, ya bayyana cewa sun karramar malamin ne kan irin gudunmawar da ya ke bayarwa kan zaman lafiya ta hanyar wa’azuzzukan da ya ke gabatarwa a gidajen rediyo da talbajin da ke Jihar Filato.
Ya ce, babu shakka jama’a su na matukar amfana da wa’zuzzukan da malamin ya ke gabatarwa. Don haka kungiyar ta zabo shi, ta karrama shi, don ta dada karfafa ma sa gwiwa kan wannan aiki da ya sanya a gaba.
‘’Daga yanzu za mu rika tuntubar Malam kan duk abinda ya shafi addinin Musulunci, wanda za mu sanya a cikin finafinan da mu ke shiryawa, domin ka rika taimaka ma na.’’
Attahiru Babayo ya yi bayanin cewa, kungiyar ta na tallafa wa al’umma, don haka a lokacin da a ka yi dokar kulle na annobar Korona a Jihar Filato ta tallafa wa mabuka da kayayyakin abinci.
Har’ila yau ya ce, a lokacin da aka aka yi rikici a Barikin Ladi a shekarun baya, kungiyar ta tallafawa wadanda rikicin ya shafa mutum 15, ta hanyar koya masu sana’ar daukar hoto.
A nasa jawabin Ustaz Abubakar Imam Bala Gana ya bayyana matukar farin cikinsa da wannan karramawa, da aka yi masa.
Ya ce, babu shakka wannan karrama zata dada karfafa masa gwiwa, kan aikin da’awar da yake gudanarwa.
Ustaz Abubakar Gana ya yi bayanin cewa addinin musulunci bai hana sana’ar fim ba. Abin da aka hana yi a fim, a addinin musulunci, shi ne a kwakwayi Allah ko Manzon Allah SAW.
‘’Akwai wadanda suke bata maku suna a wannan sana’a. kuma nasan ku kanku, bakwa jin dadin irin abin da wadannan mutane su ke yi. A kowace sana’a ana samun bata gari, don haka bai kamata mutum yace gabaki daya, fim babu kyau ba. Domin Fim sana’a ce da mutane suke yi, suna samun abin da zasu rike kansu da iyalansu’’.
Ita dai tawagar wannan kungiya da suka halarci wannan taro, sun hada da uban kungiyar Alhaji Abdu Kano wanda aka fi sani da Karkuzu da shugaban kungiyar Hamza Abubakar Talle Maifata da Alhaji Tanimu Akawu da Auwal Hassan Tubarkalla da Nasiru Aliyu da Anas Hassan Tubarkalla Maihula da Tijani Lawandi Datti da Mansur Muhammad da Rabi’u Yakubu Kwande da Hajiya Fati Abubakar da Zulaiha Ishak da kuma Nafisa Abubakar.
Advertisement

labarai