Kungiyar ‘yan kasuwan arewa reshen Jihar Kogi ta zabi sabbin shugabannin da za su tafiyar shugabancin kungiyar na tsawon shekaru hudu a jihar.
Wadanda aka zaban sun hada da Malam Umar Mohammed, a matsayin shugaba da Alhaji Yakubu Abubakar Idris, a matsayin mataimakin shugaba da Mohammed Aliyu, sakatare janar da Deborah Akambi, mataimakiyar sakatare janar da Dayyabu Iliyasu Ibrahim, sakataren kudi da Sadik Jibril, sakataren shirye-shirye da kuma Suleiman Danasabe, a matsayin ma’aji.
- Jihohin Arewa Da Suka Fi Noma Waken Soya A Nijeriya
- Kotu Ta Umarci A Kamo Mata Dogarin Gwamna El-Rufa’i
Sauren su ne; Sale Murtala, mai kididdigar kudi da Ahmed Abbas, jami’in hulda da jama’a na daya da Zayyanu Abubakar, jami’in hulda da jama’a na biyu da Toyin Daudu, shigabar mata da kuma Fumilayo Olumodeji, mataimakiyar shugabar mata.
Har ila yau, akwai Tasiu Hussain, shugaban matasa da Abdullahi Garba, Edco na daya da Nasiru Ali, Edco na biyu da Halima Nsasiru, Edco na uku da Inusa Sani, mai kayyadewa da Zayyanu Salisu, mai sa ido da Sabiu Sani Farinkaya, mai kula da kafafen yada labarai da Yusuf Mohammed Jamiu, mai ba da shawara a kan shari’a na daya, Idowu Adejumo, mai ba da shawara a kan shari’a na biyu da Ahmadu Abubakar, a matsayin sakataren mulki.
Da yake jawabi a madadin sauran shugabannin kungiyar jim kadan bayan zabarsu, sabon shugaban kungiyar, Malam Umar Mohammed ya gode wa dukkan mambobin kungiyar ‘yan kasuwan arewa, reshen Jihar Kogi da suka ba su daman jagorancin kungiyar, sannan yayi alkawarin sauke nauyin da suka dora musu. Ya nemi hadin kan ‘ya’yan kungiyar na ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.