’Yan Kasuwar Kwari Sun Koka Kan Rashin Gudanar Da Zabe

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Har yanzu ‘yan kasuwar Kantin Kwari na ci gaba da kokawa bisa rashin gudanar da zaben kungiyar ‘yan kasuwar Kwarin har yanzu bayan dogon lokaci da Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin riko da aka dora wa alhakin yin zaben.

‘Yan kasuwar sun nuna damuwa a kan jan kafa da suka ce kwamitin rikon da Gwamnatin Kano ta kafa yake yi na rashin gudanar da zaben da suka ce za su yi tun wa’adin watanni ukun farko da aka ba su, amma sai ga shi sai kara tsawaita wa’adinsu ake yi ba tare da an yi zaben ba.

Sai dai a nasu bangaren, shugaban kwamitin riko na kasuwar Kantin Kwarin Alhaji Abdullai Haruna Kwaru, ya bayyana cewa tsaikon da da aka samu ya faru ne sakamakon tsare-tsaren da suke yi na tabbatar da dora kungiyar a kan ingantattun tsare-tsare.

Ya yi nuni da cewa, zuwan kwamitinsu

ya sami nasarar yin gyare-gyare ga kundin tsarin mulkin kasuwar, wanda aka gabatar wa ‘yan kasuwa a wani taron da suka kira na masu ruwa da tsaki na kasuwar aka kuma tabbatar da shi.

Sun kuma tsara kwamitin zabe da saida takardar neman shiga zabuka ga ‘yan takara na matakai daban-daban, sannan kuma an mika sunayen ‘yan takara don tantancewa ga jami’an tsaro don kauce wa sanya wadanda ba su cancanta ba.

Alhaji Abdullahi  Haruna Kwaru ya ce, shirye-shirye sun yi nisa don gudanar da zaben nan gaba kadan, illa dai kawai ana kokarin shawo kan wasu ‘yan matsaloli ne da suka hada da wasu kudi da ake da bukatar gwamnati ta sahale musu su hada da wanda suke da shi don gudanar da zaben da zarar komai ya kammala za su gudanar da zaben.

Dagan an, ya yi kira ga ‘yan kasuwar da su dada hakuri, don kuwa kwamitin nasa na iya kokarisa wajen ganin an gudanar da zabe mai sahihi a kasuwar. Ya kuma yaba wa gwamnatin Kano bisa kokarinta na zamanantar da kasuwar Kantin Kwari ta gine-gine da ake yi na shaguna da hanyoyi da fitilu da ake sanyawa a kasuwar.

Exit mobile version