Jami’in hukumar kashe gobara ta jihar Kano sun samu nasarar ceto mutum bakwai da wata Katangar dakin adana kaya ta Sufaye da ke a birinin Kano ta rushe ta dane su.
Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya fitar a ranar Lahadi a Kano, ya ce, lamarin ya faru ne a makon da ya gabata.
- Rushe Daula: Kamfani Ya Garzaya Kotu, Kan Gwamnatin Kano Ta Biya Shi Diyyar ₦ 10bn
- Abba Gida-Gida Ya Jagoranci Rusa Wani Gini Mai Hawa 3 Dauke Da Shaguna 90 A Kano
Kakakin hukumar ya kara da cewa, sun samu rahoton faruwar lamarin bayan wani mai suna, Bashir Mansur, ya kira layin karta-kwana na hukumar da misalin karfe 05:43 na rana.
Saminu Ya ce, suna samun rahoton suka yi gaggawar tura jami’insu zuwa wajen da misalin karfe 05:47, inda ya bayyana cewa, rushewar ginun ta yi sanadin danne mutum bakwai wadanda jami’insu suka ceto su.
A cewarsa, wadanda abin ya rutsa da su duk an ceto su a raye, mutanen sun hada da Abubakar Abdullahi mai shekaru 30 da Abdulsalam Idris mai shekaru 20 sai Usman Abdullahi mai shekaru 20.
Sauran sun hada da Usaini Muhammed dan shekara 30 sai kuma Umar Isah mai shekaru 40.
Kakakin ya bayyana cewa, mutum biyar daga cikinsu da suka samu raunuka an garzaya da su zuwa Asibitin kwararru na Abdullahi Wase da ke Kano don a duba tafiyarsu.
Ya ce biyu daga cikinsu da suka samu munanan raunuka an tura su zuwa Asibitin Albarka don a duba tafiyarsu, inda ya ce ana ci gaba gudanar da bincike kan lamarin.