Hukumar samar da abinci da kula da aikin noma ta duniya (FAO), ta sanar da cewa; a halin yanzu ‘yan Nijeriya miliyan 1.8 ne ke fama da matsalar yunwa.
Karamin Ministan Ma’aikatar Noma da Samar da Wadataccen Abinci, Aliyu Sabi Abdullahi; ya sanar da hakan ne a Abuja, wajen taron manema labarai.
- MDD Za Ta Yi Duk Mai Yiwuwa Wajen Taimaka Wa Nijeriya Kawo Karshen Talauci
- Kamfanoni 80 Sun Bayyana Burinsu Na Halartar Baje Kolin CIIE Karo Na 8
Sai dai, Abdullahi ya shelanta cewa; gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen yakar rashin abinci a kasar, inda ya yi nuni da cewa; a 2023, mutane miliyan 733 ne ke fuskantar yunwa a dukkanin fadin duniya.
Ministan, wanda ya bayyana haka a bikin ranar abinci ta duniya da aka gudanar a kwanakin baya ya ci gaba da cewa, bisa rahoton yanzu da hukumar FAO ta wallafa kan karancin abinci da kuma abinci mara gina jiki da mutane ke fuskanta ya kai miliyan 733 a 2023 a fadin duniya.
Ya kara da cewa, kimanin mutane biliyan 2.33 sun fuskanci karancin abinci a 2023, inda kuma mutane biliyan 2.8 a 2022, ba sa iya samun abinci mai gina jiki.
Ya yi gargadin cewa, idan har mahukunta a kasar ba su dauki matakan da suka kamata ba, kimanin ‘yan Nijeriya miliyan 582 ne za su fuskanci rashin samun abinci mai gina jiki nan da 2030.
Abdullahi ya sanar da cewa, akwai manyan kalubale da dama da suka haifar da karancin abinci a duniya da suka hada da sauyin yanayi, fari, yawan samun ruwan sama da sauransu.
A cewar tasa, wadannan kalubalen sun kasance barazana a kan harkokin noma baki-daya, sannan kuma ya danganta da karancin abincin da ake ci gaba da samu a kasar sakamakon rashin tsaro, matsin tattalin arziki, annobar ambaliyar ruwan sama da kuma cire tallafin mai.
Sai dai, ya sanar da cewa; don mangance wadannan kalubale, wadanda kuma suka zamo karfen kafa wajen cimma burin da gwamnatin tarayya ta sanya a gaba na samar da wadataccen abinci a kasar, gwamnatin ta wanzar da sauye-sauye da dama da suka hada da kirkiro da ayyukan yi da kuma rage tsadar kayan abinci.
Ya kara da cewa, dole ne har sai masu ruwa da tsaki a wannan kasa, su ma sun bayar da tasu gudunmawar; kafin a iya kawo karshen wadannan matsaloli.
A cewarsa, a shekarar 2017; Nijeriya ta samu gagarumar nasara a fannin aikin noma a duniya, inda ta kai mataki na daya a fannin noman Rogo da Doya, inda ta noma wadannan amfani da suka kai kimanin tan miliyan 59.4 da kuma tan miliyan 47.9 baki-daya.
Bugu da kari, ya kara da cewa; Nijeriya ta kai mataki na 14 wajen noman Masara, inda ta noma tan miliyan 10.42; ta kai mataki na hudu a fannin noman Kwakwar manja, inda ta noma tan miliyan 7.7 a cikin shekara guda.
Kazalika a 2019, Nijeriya ce kan gaba wajen noman Shinkafa a dukkanin Nahiyar Afirka, inda aka noma tan miliyan tara.