DAKTA NAFISA HAYATUDDEEN kawararriyar likita ce a fannin kwakwalwa. A wannan tattaunawar da ta yi da LEADERSHIP A Yau Juma’a, ta yi bayanai masu muhimmanci da suka shafi kiwon lafiyar kwakwalwa da kuma irin ta’adin da shaye-shaye ke yi a tsakanin ‘Yan Nijeriya. Wakilinmu IDRIS UMAR ne ya tattauna da ita a ofishinta da ke asibitin masu matsalar kwakwalwa a Kaduna wato ‘Federal Neuso-Psychiatric Hospital’ a turance, ga yadda zantawar tasu ta gudana:
Likita, masu karatu za su so su ji sunanki da matsayinki a wannan asibiti?
Assalamu alaikum, sunana Dakta Nafisatu Hayatuddeen, ni kwararriyar likita ce a bangaren da ya shafi lalurar kwakwalwa da damuwa a asibitin Barnawa da ke a Kaduna.
Dakta ko za ki gaya mana takaitaccen tarihinki?
To ni dai asalina ‘yar Zariya ce, mahaifina dan Zariya ne; Injiniya Hayatuddeen Muhammed, ma’aikacin karantarwa ne gaskiya, haka kuma mahaifiyata Hajiya Indo Muhammad ita ma Malama ce ta makaranta. An haife ni ne a Zariya na yi duk rayuwa ta a Zariya, duk karatuna daga Primary, Secondary har zuwa Unibersity duk a Zariya na yi. So na gama 2008, kafin na gama karatu na yi aure, to da na gama karatun gabakidaya sai na dawo Kaduna da zama. So aikina na.likitanci dai daga 2008 na fara shi a nan Kaduna, na yi housemanship, karatu karkashin manyan likitoci farkon aiki na yi a nan asibitin Barau Dikko da ke Kaduna, bayan nan na yi bautar kasa shima a Kaduna, bayan nan tunda ra’ayina ya fi karkata ga wannan bangaren sai na samu training position zan ce ko kara kwarewar karatu na likitanci, a wannan asibiti
na gwamnatin tarayya da ke Barnawa.
Likita akwai bangarori da yawa na rayuwa da ake karatu lauya ne, tukin
jirgin sama da sauransu, me ya ba ki sha’awa kika yi karatu a bangaren
kwakwalwa?
Karatun makarantar boko da wahala dai amma Alhamdulillahi ban rika samun matsala ba sosai wajen karatu a makaranta tun da ka ga kamar faduwa ce ta zo daidai da zama, ra’ayina ya karkata wajen taimakawa al’umma musamman mata, hakan ya dada jawo ni ga karatun likitanci, to da na yi karatun kowa dai tunaninsa ka yi bangaren mata haihuwa, na yi na yi iya yina yadda zan.sa kai na yadda zan so irin nan wurin amma da ya ke ba kaddarata ba ce gaskiya, na yi kokari ra’ayina ya yi yawa a irin nan wurin gaskiya ban samu ba. To a cikin karatunmu farko in kana karatun likita za a zagaya da kai kowanne bangare, ni sai ya fado cewa sanda muka taba bangaren da ya shafi kwakwalwa da lalurai na damuwa sai a lokacin gabaki daya ya shiga raina.
Menene lalurai na damuwa?
Na damuwa da turanci ‘Mental illnesses’ muke ce masu, don mun san sun samu asali ne daga kwakwalwa, amma yadda zai fi sauki yadda mutane za su fahimta shi ne in an ce ya shafi damuwa, bacin rai ko tashin hankali, ko irin wadannan abubuwan, ‘psychological problems’ kenan, to nan ne dai inda hankalina ya fi karkata.
Daga nan kuma a cikin aikina inda nake ‘Housemanship’ na ci karo da wata mata matsala ce ta ke ta kawo ta asibiti kullum ta zo ta tafi yau lalura daban tana ta sintiri asibiti yau ta ce ciwon kai jibi ciwon jiki an yi test an yi test ta sha magani ta sha magani lalura ta ki warkewa.
Wata rana da na gan ta sai na ce Malama ko dai akwai wani abu da ke damunki ne? Sai ta fashe da kuka, to daga nan sai da magana ta kai ga na ba ta lokaci daban na ga duk wanda zan gani muka zauna muka yi magana wajen awa biyu. sai na fahimci cewa damuwa ce ta yi mata yawa a rai, ba ta da wanda za ta fada wa ba ta san yadda za ta yi ba. Ya taru ya yi mata tsanani har ya sa ta kamu da wata lalura da muke kira ‘Depression’. To wannan depression din shi ne ya sa ta ke ta yawon asibiti yau ta ce kaza gobe ta ce kaza.
Shi menene depression din?
Shi Depression lalura ce ta kwakwalwa, amma akasari ta kan dakko sila daga damuwa ta yau da kullum, al’amuran da ba su tafi daidai ba a rayuwar mutum ko kuwa wasu al’amura na jarabawa a rayuwar mutum, ya rikita mutum ya tada wa mutum hankali, to daga nan ne sai wannan lalura ta bayyana. Ta kan bayyana da kunci, tsananin kunci wanda ya ma fi
karfin lalurar da mutum ke ciki, misali yau da kullum abin bacin rai zai faru, rai zai baci hala ma ranar ba za ka yi barci sosai ba ya dan dame ka, gobe ka ji ya yi sauki jibi ka ji ya dan kara sauki.
To ita wannan lalura in ta shiga maimakon bacin ran ya rika sauki sai ya yi ta cigaba, bakin ciki dai bakin ciki, wani sai ya yi ta yawan kuka daga nan wani sai ya yi tunanin gara ma ya mutu ya huta, yana ganin rayuwarsa babu wani kyau da za ta yi. Bai tuna komai bai tunanin
komai sai abubuwa munana, to duk wannan alamomi ne da suka shafi depression.
Wasu ya kan hana su barci, ko kuma da ya yi barci ya farka shike nan babu sauran wani barcin, rashin cin abinci shi ne za ka ga wani ya rame in ka gan shi za ka ce lafiya kuwa. Shi ba zai ce ga wata lalura da aka auna shi a asibiti aka ce yana da ita ba, to amma kuma depression din ce. To ganin wannan mu’amala da na yi da wannan mata sai na ga to in haka ne mata nawa muke gani kullum suna sintiri a asibiti a yi ta shan magani amma kuma ga inda matsala ta ke.
Wane kalubale kika fuskanta tsakanin fara karatunki zuwa wannan lokacin?
To abin da zan ce dai bai wuce kalubalen yadda za ka yidaidaita hidimomin yau da kullum da daukar naye-nauye yadda za ka dauke su duka ka kuma hada da aiki, ga ‘ya’ya, ga iyaye, ga biki, ‘yan uwa, ga kuma wannan aiki ga karatu, kullum wannan aiki, ga aiki ga kuma karatu saboda wannan karatun bai fi shekara biyu da ta wuce na gama kwarewa ba. Tun 2000 na shiga ABU, kusan shekara goma sha, a wannan lokaci kusan kullum cikin karatu nake, kullum akwai nayin, to wannan shi ne babban kalubale da zan ce na fuskanta gaskiya, kuma Alhamdulillahi, babban abin da ya taimaka min shi ne ina samun kulawa da tallafi da ba da karfin gwiwa daga dukkan wasu ‘yan uwana,Gaskiya kowa da ke zagaye da ni ya bayar da tashi gudummuwar; miji, tun farko dama mai burin son in yi karatu ne duk iya abin da nake so bai taba nuna fushi ba, ba ya hanawa duk jarabawa in zan je mu kan tafi jarabawa mu je Ibadan.
Wani karatun za mu je Abuja mu je Legas, mu je ina ne, duk inda za ni in dai da hali zai bini, wani lokaci zai dauki hutu daga aiki mu je tare don dai abin ya yi min sauki, sanda na ke karatu farko a makaranta a ABU kafin na yi Digiri, lokacin na yi sa’a iyayena a Zariya suke, su ma sun taimakamin don tun ina makaranta na fara haihuwa, to ga goyo ga karatu, ga hidimar miji, miji ba a gari ba, to iyayena sun bani karfin gwiwa da taimakawa gaskiya, gaskiya Alhamdulillahi wannan taimako da nake samu shi ne ya kawo abin da sauki.
To Dakta, ban sani ba yanzu wane kalubale kuke fuskanta na wadannan
masu ciwon hauka?
Akwai kalubale iri-iri, ya danganta da inda ka duba al’amarin, mafi akasari babban kalubale da muke samu ka ga mutum yau na farko kafin ma mutane su gane cewa wannan lalurace ta kwakwalwa, da akwai gurin magani matsala ne, shi kansa, saboda mafi akasari a al’ummarmu haka mutum zai ta yawo da lalura da ta shafi kwakwalwa, amma sabida babu fadakarwa babu sani cewa wannan lalura ce fa da ake iya magance ta a asibiti, to sai a yi ta yawo a yi na gargajiya a yi na rubutu, duk a je a yi ta ta yi, sai ka ga wani abin kafin a gane din a zo asibiti sai a yi ta wahala, sannan kudi sun kare, karfi ya kare ciwo kuma ya dade, lalura kuma
irin wannan duk kwanakin da take karawa ba a dauki mataki da wuri ba to kata lalata kwakwalwa ta ke yi, yadda ko da an fara maganin daga baya yanayin saukin da ake samu ba kamar in an tari abin da wuri ba, shi kansa kalubale ne.
Wani za ka ga an kawo ga lalura ta kai inda ta kai, ana son a kwantar ana son a yi magani amma kuma ba kudin, gwamnati ba daukar dawainiya ta ke ta masu ciwon kwakwalwa ba, don haka duk dawainiya na karewa ne kan ‘yan uwa, ka tuna mai lalurar kwakwalwa kuma irin wannan mafi akasari ba iya aiki suke yi ba, to wani ya shekara hudu zuwa biyar da lalura ko da aiki ya ke yi da yana sana’a duk abin da ya tara ya kare wajen magani, to suma kuma ‘yan uwan da za su dakko mutum su kawo shi wajen magani su ma kuma sun bar sana’ar da suke yi da aikin da suke yi ka ga an yi rashi biyu, sannan a kare a kawo mutum a ce kuma duk da haka kudi ake bukata. To wannan yana takura aikinmu yana hana aikinmu ya tafi daidai.
Bugu da kari al’ummarmu ba ta son yarda cewa wannan ciwo fa na kwakwalwa ne, an fi son dai a ce a’a aljannu ne, a’a sihiri aka yi, a’a jifa ne, ko kuma a’a maita ce, an fi sha’awar irin wannan an fi son irin wannan. Shi ya sa mafi yawa ko da suna zuwa nan din suna yin na asibitin sai a hada da na gida, maimakon a maida hankali kan guda daya.
An yi shekara da shekaru ana wancan ba a samu galaba ba, an zo an fara wannan an fara samun sauki, gaskiya in mutum ya zo in irin lalurar da mutum da wuya ya warke ne za mu gaya maka, ba za mu boye ma maka ba, za mu gaya maka wannan lalura ce da za ta bukaci a yi ta shan magani hala ma wani har karshen rayuwarsa, to amma mutane basu son jin haka sun fi son dai a ce an warke shike nan, in kuma ka duba yau da kullum a rayuwa akwai lalurar da ba a warkewa misali; hawan jini, ciwon siga, ko HIB, lalurai ne da in dai kana shan magani kana kula da kanka babu abin da zai hana ka gudanar da rayuwarka ka samu rayuwa mai inganci. To amma kuma saboda wata kyamata da ake yi ne da kyara da ake yi ga masu cutar da ta shafi kwakwalwa ake kyamatarsu to shi ne mutane ba su so a danganta su da wannan lalura, shi ne sai a yi ta bi a ce an je wajen wancan Malami addu’a, an gwada wancan rubutu menene da menene, wadannan sun shafi kalubalen da muke fuskanta gaskiya.
To yanzu Dakta za ki ga akwai yawan amfani da kwawoyin da suke sa
lalura a kai, ban sani ba a shekara kukan karbi mutum nawa?
Bisa kimantawa gaskiya yanzu ita dai wannan matsala ta shan kayan maye da suka shafi wannan larura babbar matsala ce da ta buwaye mu gaba daya al’ummar Nijeriya. Binciken da aka yi na baya bayan nan da ya fito, a cire masu shan taba sigari da giya, wanda suka ce sun sha wani abu, a shekarar da ta wuce, bayan sigari bayan giya, kusan kashi 15 cikin 100 na mutane, idan Nijeriya muna da mutum miliyan 200 in ka kimanta kashi 15 cikin 100 misali, zai zama kusan mutum miliyan 30 kenan.
Miliyan 30 a cikin mutum miliyan 200, ka ga kuwa ai mutane da yawa kenan suna shan kayan
maye. To a cikin kuma wanda zai iya har ya shafi kwakwalwa akwai su da yawa don shi kan sa shan kayan mayen ita kanta lalurace ko da mutum bai fara ihu yana tube kaya ba, a yadda ya ke tafiyar da rayuwarsa.
A kan ga dan canji ba kamar wanda bai mu’amala da komai ba. Akwai canji a yadda ya ke mu’amala, da yadda ya ke sana’a, da yadda ya ke sarrafa kudi, a addini ko rike gaskiya. To ka ga duk wannan ya shafi inganci na rayuwar mutum, a tantance a ce ga yawan wadanda muka gani kayyade su zai yi wuya, amma kuma abu mai muhimmanci shi ne ina ga a fahimci ya buwayi ko ina akwai shi a al’ummarmu, iya wanda za mu iya shi ne wanda ya zo wurimmu amma gaskiya ana bukatar dokoki ne da gwamnati, da kungiyoyi masu zaman kansu da
Malamai da iyaye da shuwagabannin addini mu fahimci cewa wannan matsalar ba karama ba ce, in ta tsallake kan ka to tana nan gidan makocinka, in ta tsallake makocinka to tana nan gidan dan uwanka, to mu sani cewa wannan matsala ce da ta ke tare da kowa a cikin al’ummarmu, sai mun tashi tsaye mu ga abin da da za mu iya.
To Dakta a tambaya ta kusa da ta karshe, a lokacin da ki ka ga za ki
iya ba da gudummuwarki a wannan fannin, akwai wata nasara da ba za ki
taba mantawa da ita ba?
Ai ina ga babbar nasarar da zan ce na samu shi ne kwanciyar hankali, dan zan ga samun ka shiga wuri da kai a ranka abin da ka ke so kenan, don na ga kawayena da yawa da muka yi karatu sun nemi su kware a fannin da ba nan suke so ba a zuciyarsu tun farko. Kawai dai sun yi
shi ne saboda shi ya fi sauki hala a garin da suke zama, shi ne akwai zai fi ma rayuwarsu sauki, mazajensu ba za su yi korafi ba. Babbar nasara da zan ce kenan na samu, to amma baya ga nan, akwai abubuwa daban-daban da suka taso a yanayin aikina da kuma karatuna, kamar yadda na ce fadakarwa kan ma su fahimci akwai laluran da ake iya samun sauki akwai wanda har warkewa ake yi.
Daga nan muna sallamarsu mu ce su daina shan magani, to da na fahimci matsala ce babba a al’ummarmu don kaina sai na ke ba da lokaci na, in ya shafi fadakarwa haka cikin yaren Hausa kamar shirin gidan Radio. haka nakan je in yi. Sai na je na yi bayanai a kan kowacce larura, na yi bayanai a kan depression din nan a kafafe daban daban, na yi bayanai a kan farfadiya da sauran lalura masu kamari da suka shafi wannan larura da dama.
Wani abu da na tuno likita, da yawa wasu kan ce wai likitan kwakwalwa
suma kamar mara lafiyar suke, me za ki ce game da hakan?
Wallahi wannan shi mu ke ce ma ‘Stigmatizing attitude,’ kawai mutane ne suke ganin kamar haka ne amma ba haka ba ne, a ce wai dole sai ka zama mai karancin hankali sannan za ka gane mai karancin hankali wallahi ba haka ba ne ba, ai karatu ne, ilimi ne, in kuma ka nemi wannan ilimin za ka gane za ka sani, za ka gane kuma wacce irin matsala ce domin ka taimaka mashi, duk abin da mutum ke fadi da ya fita hankali za ka gane.
Duk irin wannan har yanzu suna tasiri, ni kaina da na yanke shawarar zan yi wannan karatun sai da wata ta ce min ke da masu lafiya ma likitoci ba su ishe su ba bare mahaukata, Na ce to ai su ma mutane ne. Mutane ne, kuma babu wanda ya fi karfin wannan lalura ta kama shi, in ba ta kama ka ba ta kama dan ka, kuma kai ma tunda ba ka gama rayuwa ba, tana iya kama ka a tsufanka,don haka babu mai riga-kafi. In kai ne in ta kama ka za ka so a kyamace ka, zan so in ina mace in ina da lalura in na je asibiti in ga mace Musulma iri na ‘yar Arewa wadda in na yi bayani za ta fahimce ni daga inda na ke, in kuwa mu bamu sadaukar da kanmu mun yi ba, to ya za mu taimakawa saura daruruwan da suke fama da wannan matsalar. Duk irin wadannan abubuwan har yanzu akwai su.
Na gode sosai