Mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya koka kan irin caccakar da ake yi wa shugaba Buhari.
Ya ce ba a nuna kauna ga shugabanni a lokacin da suke kan mulki.
- PDP Ta Dakatar Da Shugabanta Na Kasa Kan Zargin Yi Wa Jam’iyyar Adawa Aiki
- Wani Mutum Ya Yi Wa ‘Yarsa Ciki, Ya Yi Barazanar Kashe Ta A Ogun
Ya bayar da misali da zamanin mulkin Goodluck Jonathan, wanda ya ce mutane sun yi ta sukarsa amma a yanzu, ya zama mutumin da ‘yan Nijeriya da dama ke yabo.
Garba Shehu, ya ce irin haka za ta faru idan Buhari ya mika mulki ga shugaban kasa mai jiran gado.
Game da manufar takaita amfani da tsabar kudi, Garba Shehu ya ce tsarin na gwamnati mai ci abin so ne don haka ba za a soke shi ba.
A cewarsa, “takaita amfani da takardun kudi ci gaba ne ga ‘yan Nijeriya saboda kasashen da suka ci gaba tuni suke tafiya a kan wannan tsarin”.
Gomman mutane sun fuskancu matsaloli saboda karancin takardun kudi tun bayan da gwamnatin tarayya ta bijiro da tsarin sauya fasalin takardun kudin.
Sai dai a ranar Juma’a da ta gabata Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya saki kudi, sannan kuma ya umarci bankuna da yi aiki a kwanakin mako don wadata mutane da kudin.
Tuni dai takardun kudin suka fara yawo a hannun mutane, inda bakunan kasuwanci da dama suka bi umarnin na CBN.