Connect with us

RIGAR 'YANCI

’Yan Sanda Na Cigiyar Iyayen Yaran Da A Ka Sato

Published

on

A ranar Litinin din nan ce, ‘Yan sanda a Abuja, suka yi kira ga al’umma musamman wadanda su ke cigiyar ‘ya’yansu da su zo ofishin ‘yan sandan domin su tantance wasu satattun yara uku da su ke a hannun ‘yan sandan tun daga watan Yuni kawo yanzun.

Yaran sun kunshi ‘yan mata guda biyu da kuma namiji guda daya.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, DCP Frank Mba, ya ce yaran uku suna cikin yara shida ne da jami’an binciken sirri suka sami nasarar ceto su a wani yunkuri da suka yi lokacin da suka sami rahotannin satan yara.

Mba ya ce, tuni an ma kama wadanda suka sato su din har ma an kai su kotu an yanke masu hukunci.

Ya ce ya zama wa rundunar tilas ne da ta nuna hotunan yaran uku ko iyayen na su za su shaida su.

“Mun iya gano iyayen sauran yaran uku daga cikin su shidan, kuma tuni ‘yan sanda sun hannanta su a hannun iyayen na su,” in ji Mba.

“Sai dai abin takaici har ya zuwa yanzun ba mu iya gano iyayen wadannan ukun ba.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: