ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, November 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan sanda Sun Cafke Waɗanda Ake Zargi Da Satar Mutane A Abuja

by Muhammad
2 years ago
'Yan sanda

Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta ce ta kama mutum 16 da ake zargi da aikata miyagun laifuka da kuma garkuwa da mutane a Abuja, babban birnin ƙasar.

BBC ta rawaito cewa, hakan ya biyo bayan kaddamar da rundunar ‘yan sanda ta musamman da Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Kayode Egbetokun, ya yi kwanan nan, inda har suka samu nasarar kama mutanen da kwato makamai da alburusai a babban birnin tarayya Abuja.

  • Masu Garkuwa Sun Buƙaci A Biya Su Fansar Miliyan 30 Kan Mutanen Da Suka Sace A Abuja
  • ‘Yan Bindiga Sun Sake Garkuwa Da Matar Shugaban Fulani A Abuja

Wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan ta Nijeriya, Muyiwa Adejobi ya fitar, ya ce rundunar haɗin gwiwa ta jami’ansu sun kuma kama wasu mutum 13 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.

ADVERTISEMENT

Daga cikin waɗanda aka kama a ranar Asabar ɗin, akwai wasu masu garkuwa da mutane uku, waɗanda kuma ake zargi da aikata fashi da makami a karamar hukumar Bwari da sauran sassan Abuja.

“Daga cikin nasarorin da aka samu akwai yadda aka dakile wani shirin yin garkuwa da mutane ta hanyar leken asiri wanda ya yi sanadin kama masu garkuwa da mutane a Bwari, da kwato makamai daga hannunsu,” in ji sanarwar.

LABARAI MASU NASABA

Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola

Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa

Haka-zalika, ƴan sandan sun cafke wani mai sayar da bindigogi mai suna Everest Magaji, a lokacin da yake tattaunawa da wasu gungun ‘yan bindiga da ake nema ruwa a jallo a yanzu, domin sayar musu da muggan makamai da alburusai.

Sun ce sun kwato bindiga kirar pistol guda 11, da kuma ta harbi ka ruga biyu daga hannun wanda ake zargin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola
Manyan Labarai

Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola

November 15, 2025
Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa
Manyan Labarai

Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa

November 15, 2025
Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70
Da ɗumi-ɗuminsa

Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70

November 14, 2025
Next Post
Abin Da Ya Sa Ban Hadu Da ‘Kan-ta-waye’ Ba Lokacin Da Na Shiga Fim – Sani Abubakar

Abin Da Ya Sa Ban Hadu Da ‘Kan-ta-waye’ Ba Lokacin Da Na Shiga Fim – Sani Abubakar

LABARAI MASU NASABA

Wakilai Daga Jihohi 19 Sun Isa Ibadan Don Taron PDP Na Ƙasa

Wakilai Daga Jihohi 19 Sun Isa Ibadan Don Taron PDP Na Ƙasa

November 15, 2025
Daliban FUTA 240 Sun Samu Digiri Mai Daraja Ta Daya

Daliban FUTA 240 Sun Samu Digiri Mai Daraja Ta Daya

November 15, 2025
Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika

Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika

November 15, 2025
Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola

Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola

November 15, 2025
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje

November 15, 2025
Fashi Da Makami: An Yanke Wa ’Yan Nijeriya Hudu Mazauna Birtaniya Hukuncin Daurin Shekara 55 A Gidan Yari

Fashi Da Makami: An Yanke Wa ’Yan Nijeriya Hudu Mazauna Birtaniya Hukuncin Daurin Shekara 55 A Gidan Yari

November 15, 2025
Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa

Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa

November 15, 2025
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

’Yansanda Sun Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Ta’adda Ne A Jihar Kebbi

November 15, 2025
Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

November 14, 2025
NAHCON Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Kula Da Shafin Nusuk Masar Na Hajjin 2026

NAHCON Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Kula Da Shafin Nusuk Masar Na Hajjin 2026

November 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.