‘Yan Sanda Sun Ceto Mutum Hudu Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Abuja

Rundunar ‘yan sandan Abuja a ranar Litinin sun bayyana cewa sun yi nasarar ‘yanto mutane hudu daga hannun masu garkuwa da mutane a dutsen Sauni dake Lambata iyakar Abuja da jihar Neja.

Kakakin ‘yan sandan Abuja, DSP Anjuguri Manzah shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce mutanen da suka ceto sun samu nasarar hakan ne bayan wata samame da ‘yan sandan suka kaddamar.

Rundunar ‘yan sandan sun tabbatar da cewa; sun kuma yi nasarar korar masu garkuwa daga sansaninsu dake dutsen Sauni din.

Manzah ya ce sun kuma kai wannan samamen a sansanin masu garkuwa da mutanen ne sakamkon kiran wayar da suka samu a ofishin ‘yan sanda na Gwagwalada, inda aka ce musu an sace mutum biyu wanda ya hada mace da na namiji a gidansu a ranar 8 ga watan Fabarairu.

Manzan ya ce sun yi musayar wuta da masu garkuwa da mutanen, inda masu garkuwa suka gudu suka bar wadanda suka sato. Manzah ya ce biyu daga cikin wadanda suka ceto wanda ya hada da; Alhaji Umaru Salihu da Mariam Umaru an sato su ne daga kauyen Pagada a ranar 8 ga watan Fabarairu.

Sauran kuma sun hada da Zilkifilu Usman da Usman Shuaibu sun shaida wa ‘yan sandan cewa an sato ne daga jihar Neja a ranar 2 ga watan Fabarairu a yayin da suke kan hanyar tafiya.

 

 

 

 

Exit mobile version