Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kebbi ta kaddamar da ofishin rajistar motoci ta na’urar zamani (CMR) domin yaki da masu aikata miyagun laifukan satar abin hawa.
Bukatar yin rajistar motocin na kunshe ne a cikin wata takardar manema labarai mai dauke da sa hannun kakakin rundunar ‘Yan sandan Jihar Kebbi, SP Nafi’u Abubakar, inda aka raba wa manema labarai a Birnin Kebbi.
- Farashin Kayan Abinci Ya Ƙaru A Jihohin Nijeriya 36, Abuja, Kano, Borno Farashin Kaya Ya Sauka
- Gidauniyar M-TECH Ta Tallafawa Yara Mabukata 400 Da Tallafin Karatu A Jihar Kebbi
Kazalika takardar ta kara da cewa, “A bisa shirin babban sufeton ‘Yan sanda na 22, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, NPM, Ph.D, na inganta harkokin tsaro a cikin gida Nijeriya, rundunar ‘yansandan jihar Kebbi ta bayar da umarnin kaddamar da babban ofishin yin rigistar motocin ta na’urar zamani wato ‘Digitalized Central Motor vehicle Registry (CMR)’ da ke Hedikwatar Rundunar a Gwadangaji, da ke a Birnin Kebbi.
Haka kuma ta kara ta cewa an yi shi ne don magance laifukan da suka shafi abubuwan hawa da nufin inganta lafiyar jama’a da tsaron mutanen jihar Kebbi.
Takardar ta ci gaba da cewa, duba da yadda manyan laifukan da suka shafi motoci ke karuwa, rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta sake farfado da babban ofishin rajistar motoci ta hanyar sanya shi a cikin na’ura mai kwakwalwa ta yadda za a rika amfani da bayanan mota guda domin ya ba da hakikanin bayanai daga ’yansandan a yayin gudanar da bincike na zamani wajen kokawa da laifukan satar motoci a fadin jahohin kasar nan.
Har ilayau, kaddamar da ofishin rajista yana da fa’idodi masu yawa, waÉ—anda suka haÉ—a da; inganta tsaro da samun bayanai na kai-tsaye daga na’urar CMR ga ‘yan Æ™asa, haka kuma za su iya samun babban kwarin gwiwa ga tsaron motocinsu.
Haka kuma ingantattun bayanan abin hawa za su taimaka wajen dakile wa da magance laifuka satar motoci cikin sauki, da nufin tabbatar da cewa, an kiyaye kadarorin ‘yan kasa.
Hakazalika, ‘Yan sandan za su kasance mafi kyawun kayan aiki don aiwatar da dokokin da suka shafi motoci, kamar rajista da lasisi. Hakan zai haifar da samar da ingantattun hanyoyi da inganta hanyoyin tafiyar da ababen hawa da za su amfanar da duk masu amfani da ababen hawansu a kan hanya.
Bugu da kari takardar ta ce cikakkun bayanai na motoci za su zama abin hana masu aikata laifuka waÉ—anda za su iya amfani da ababen hawa don ayyukan da ba su dace ba. Sanin cewa jami’an tsaro na da damar samun ingantattun bayanai na iya hana aikata laifukan satar motoci a jahohin kasar nan.
Don haka Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kebbi, CP Chris Aimionowane, psc, mnips, ya bukaci al’ummar Jihar masu son zaman lafiya da su rungumi shirin na IGP na kawo sauyi ta hanyar yiwa motocinsu rajistar ta na’uran zamani da nufin bayar da gudunmawarsu tare da inganta tsaro na cikin gida da tabbatar da tsaro ga kowa da kowa.
Daga karshe don yin rijistar motar ku, ku ziyarci https://cmris.npf.gov.ng ko tuntuÉ“i Jami’in da ke kula da ofishin yin rigiata a rundunar ‘yansanda ta jihar akan wannan Lamba 08062118443 ko don neman karin bayani.