Rundunar ‘yan sandan jihar Edo a ranar Lahadi ta ce jami’anta sun kama wasu mutane bakwai da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne a jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakiyar kakakin ‘yan sandan jihar, ASP Jennifer Iwegbu, wadda aka rabawa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) a Benin.
- Ban Taba Umartar Kiristoci Su Sayi Bindiga Ba — Fasto Adeboye
- PDP Reshen Jihar Osun Ta Koka Kan Yadda ‘Yan Sanda Ke Yi Wa ‘Ya’Yanta Dauki Dai-dai
NAN ta ruwaito cewa rundunar ‘yan sanda a ranar Juma’a ta kama tare da gabatar da ‘yan kungiyar asiri bakwai, wadanda ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne na Eiye da Aiye.
Iwegbu ta bayyana sunayen wadanda ake zargin Andrew Owhoyavwosa mai shekaru 22 da Joseph Meshak mai shekaru 25 da Osazee Solomon mai shekaru 35 da Godswill Obasohan mai shekaru 25 da Charles Odiase mai shekaru 52 da Okoh Peter mai shekaru 68.
An kama su ne a hannun Ekiadolor a cikin al’ummar Ekowe, yayin da na bakwai kuma an kama su ne a hanyar Igbe da ke karamar hukumar Auchi Etsako ta yammacin jihar.
A cewarta, an kama su ne kan irin kisan wuce gona da iri a jihar Edo da suke yi.
“A ranar 02/07/2022, jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Edo, reshen Ekiadolor, a yayin da suke sintiri a cikin garin Ekowe da kewaye, sun kama wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne a gidan matasan unguwar.
“Wadanda ake zargin, da ganin jami’an ‘yan sandan, sun yi taho-mu-gama ne daga wajen taron da suka yi ba bisa ka’ida ba.
“Wannan matakin ya ja hankalin jami’an ‘yan sanda inda suka fatattake su wanda hakan ya sa aka kama mutanen shida.
“A wajen binciken da aka gudanar a wurin ya kai ga gano bindigogi guda biyu da aka kera a cikin gida, harsashi masu rai guda 30, akwatin bayar da agajin gaggawa guda daya, Kolanut, kwai, shanu, mushen kaza guda, wayoyin hannu da tsabar kudi Naira dubu talatin da bakwai,”