‘Yan Sandan Duniya Sun Kai Sumame Mafi Girma Kan Masu Laifi

Wani gagarumin sumame da ‘Yan Sandan duniya suka kaddamar a Kasashe 33 tare da hukumar da ke yaki da masu amfani da kwayoyin da ke kara kuzari, yayi nasarar kwace miliyoyin magungunan da aka haramta amfani da su, tare da kama mutane 234.

Rundunar Yan Sandan Turai da ake kira Europol ta ce aikin ya shafi Kasashe 23 da ke Turai da kuma 10 a sauran sassan duniya da suka kunshi Albaniya da Kwalambiya da Iceland da Switzerland da kuma Amurka.

Rundunar ta Europol ta ce adadin haramtattun magungunan da hadin gwiwar jami’an tsaron suka yi nasarar kwacewa yayin sumamen ya kai kusan miliyan 4.

Rundunar ta kuma ce yayin gudanar da aikin, sun yi nasarar tarwatsa kungiyoyin tsageru masu aikata laifuffuka 17 da ke safarar wkayoyin a Turai. Kasar Italiya ce ta jagoranci sumamen mafi girma da rundunar ‘Yan Sandan ta duniya ta kai kan masu laifi a Kasashe da dama.

Exit mobile version