A tsakanin shekarar 2011 zuwa 2019, ‘yan ta’adda a Zamfara sun karbi sama da Naira biliyan 3 a matsayin kudin fansa daga mutane 3,672 da suka yi garkuwa da su, kamar yadda wani rahoto da gwamnatin jihar Zamfara ta bayar ya bayyana.
A cewar rahoton, kwamitin da gwamnati ta kafa a shekarar 2019 domin duba halin rashin tsaro a jihar na ayyukan kungiyoyin ‘yan ta’adda da aka fi sani da ‘yan bindiga, sun kuma raba mutane 190,340 da Muhallansu.
Kwamitin wanda shugaban ‘yan sanda mai ritaya ya jagoranta, ya kuma bayyana cewa mata 4,983 ne aka mayar zawarawa yayin da yara 25,050 suka zama marayu sanadin kashe mazajensu da iyayensu da ‘yan ta’addan suka yi a tsakanin wannan lokacin.
Rahoton ya kara da cewa fulani makiyaya an sace musu shanu kimanin 2,015, tumaki da awaki 141, da jakuna da rakuma 2,600 yayin da motoci 147,800 da suka hada da babura da sauran su aka kone ko kuma aka lalata su a cikin wannan lokacin.
Biyo bayan karuwar tashe-tashen hankula da sace-sacen mutane domin neman kudin fansa a jihar, gwamnan jihar, Bello Matawalle, ya kafa kwamitin karkashin jagorancin tsohon sufeto-Janar na ‘yan sanda, Muhammad Abubakar, a shekarar 2019, domin duba matsalar rashin tsaro a jihar tsakanin watan Yunin 2011 zuwa Mayu. 29 ga Fabrairu, 2019. Kamar yadda premium times ta rahoto.
Sai dai ana ta Ikirarin, gwamnatin Zamfara ta ce tun lokacin da Matawalle ya zama gwamna, ya magance matsalar rashin tsaro sosai a jihar.