ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Ta’adda Sun Sake Sace Mutane 87 A Wani Sabon Hari Da Suka Kai Kaduna

by Muhammad
2 years ago
Kaduna

Masu garkuwa da mutane sun sake kai wani mummunan hari a kan wasu mutane a Kajuru- Station da ke karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, inda suka yi garkuwa da mutane 87 a daren ranar Lahadi.

Harisu Dari, daya daga cikin matasan tashar Kajuru, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa ‘yan ta’addar sun kai harin da misalin karfe 10 na dare.

  • Mahara Sun Sace Dalibai 200 A Kauyen Kaduna
  • Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 9, Sun Yi Garkuwa Da 20 A Kaduna

Rahotanni na cewa, maharan ba kawai sun yi awon gaba da mutane kadai ba ne, sun yi barna, inda suka shiga shaguna jama’a tare da kwashe kayan abinci da sauran kayayyaki.

ADVERTISEMENT

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan hari da suka kai na sace mata 15 da wani namiji a yankin Dogon-Noma kwanaki kadan kafin wannan harin.

A kwanakin nan dai kananan hukumomin Kajuru da Chikun suna fuskantar sace-sacen jama’a daga mahara, wanda hakan ya jefa jihar cikin wani yanayi na tashin hankali.

LABARAI MASU NASABA

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Dari, wanda al’amarin ya tayarwa da hankali, ya bayyana irin tashin hankalin da mutanen kauyen suka shiga a sakamakon harin na ‘yan bindiga.

Dari, ya jaddada bukatar gwamnati da ta dauki matakan gaggawa wajen dakile hare-haren ‘yan bindigar, yana mai bayyana cewa har zuwa safiyar yau Litinin, ba a tuntubi mutanen yankin da aka sace ‘yan uwansu ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu
Manyan Labarai

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani
Manyan Labarai

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Manyan Labarai

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Next Post
‘Yan Bindiga Sun Kashe Wani Basarake Bayan Garkuwa Da Shi A Jihar Bauchi

‘Yan Bindiga Sun Kashe Wani Basarake Bayan Garkuwa Da Shi A Jihar Bauchi

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.