‘Yan takaran gwamnan Jihar Gombe su takwas daga jam’iyyun adawa daban-daban sun mara tazarcen gwamnan Jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya baya, tare da yin alkawarin taya shi aiki don samun nasara a zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi da ke tafe ranar Asabar.
Shugaban gamayyar tuntuba tsakanin jam’iyyun siyasa na jihar (IPAC) kuma dan takaran gwamna na Jam’iyyar Zenith Labour Party, Muhammad Gana Aliyu shi ne ya bayyana hakan yayin wata zantawa da manema labarai a ofishin sa dake Gombe.
- Dan Bindiga Ya Shiga Hannu, Ya Bayyana Yadda Ya Kashe Mutum 15 A Katsina
- Kotu Ta Daure Tsohon Kwamishina Shekara 3 Kan Almundahanar Miliyan 180 A Imo
Ya ce, sun dauki matakin ne bayan doguwar tattaunawa da nazari kan nasarorin da gwamnati mai ci ta samu a karkashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.
Ya ce, “Mun cimma wannar muhimmiyar matsaya ce bayan da muka yi nazari sosai kan yadda Gwamna Inuwa yake gudanar da ayyukan sa musamman ta fuskar samar da zaman lafiya, da tsaro da ilimi, da kiwon lafiya, da samar da ababen more rayuwa da ayyukan jinlai a faɗin jihar”.
Shugaban na IPAC ya ce, ‘yan takaran da suka mara baya ga gwamnan na Gombe kuma dan takaran gwamna na Jam’iyyar APC su ne: Muhammad Gana Aliyu na Jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP), da Sulaiman Abubakar Sunusi na Jam’iyyar National Rescue Movement (NRM), da Sadiq Abdulhamid na Jam’iyyar Boot Party (BP) da Adamu Muhammad na Jam’iyyar Action Peoples Party (APP).
Sauran sun hada da Sulaiman Jibrin na Jam’iyyar Action Democratic Party (ADP), da Adamu Aliyu Ɗanmakka na Jam’iyyar African Action Congress (AAC), sai Kelmi Jacob Lazarus na Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) da Muhammad Bello Abubakar na Jam’iyyar Allied Peoples Party (APP).
‘Yan takaran sun kuma yi kira ga magoya bayan su dasu zabi Gwamna Inuwa Yahaya don ba shi damar dorawa kan yunkurin sa na samar da ayyukan ci gaba mai ɗorewa a jihar.
‘Yan takaran gwamnan takwas da suka amincewa Gwamna Inuwa suna daga cikin ‘yan takara 13 da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya wadda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa (INEC) da hadin gwiwar Kwamitin Tuntuba Tsakanin Hukumomi Kan Harkokin Tsaro (ICCES) suka shirya a ranar 15 ga watan Fabrairun wannar shekara.