Wata kungiya da ta kunshi kwararrun ma’aikatan gwamnati da kamfanoni da ke Kano da Jigawa (KJPF) ta gudanar da wani taro tare da wallafa wani kundi da zai kasance jagora ga dukkan ‘yan takarar da suka samu nasara a jihohin.
Kungiyar dai tana karkashin shugabancin Dakta Shamsudeen da Hon Sani Zoro ta wallafa wannan kundin ne domin ya zama jagora ga ‘yan takarar da suka samu nasarar cin zabe a Kano da Jigawa wajen ciyar da jihohi gaba ta kowani fanni, inda ta gayyaci daukacin ‘yan takara masu neman mukaman siyasa da ke Kano da Jigawa.
- An Cimma Sakamako Guda 1339 Yayin Taron CIFTIS
- Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Riba Ce Ga Kasashe Masu Tasowa
Taron ya gudana ne a dakin taro tunawa da Malam Aminu Kano da ke Unguwar Gwammaja a birnin Kano.
Taron da ya samu hallartar ‘yan takarar karkashin jam’iyyu daban-daban da suka hada da dan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar APC, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, da dan takarar dan majalisar wakilai a mazabar Gezawa da Gabasawa, Hon Mahmoud Muhammad Santsi sun bayyana gamuswarsu da wannan taro da kuma yin alwashi yin aiki da wannan kundi.
Shi ma dan takarar gwamna Kano a karkashin jam’iyyar SDP, Hon Bala Muhammad Gwagwarwa da mataimakinsa Hon Habibu Sabo Dundu sun nuna gamsuwarsu game da wannan taro.
Hon Dundu ya bayyana takararsu a SDP ta gaskiya ce babu neman ganin bayan wani dan siyasa ko mai mulki a takararsu.
Ya ce jam’iyyyar SDP canji kawai take son kawo a Jihar Kano da kuma kasa baki daya. A nasa bangren, Injiniya Abba Kabir Yusuf wanda ya samu rakiyar mataimakinsa a takara, Hon Abdulsalam Gwarzo da dan takarar sanata a Kano ta Kudu, Hon Abdurrahman Kawu Sumaila da sauran jiga-jigai a jam’iyyar NNPP ya nuna cewa Kano ta dade tana bukatar irin wannan tsari na KJPF domin ci gaban Kano.