Matasan ‘yan wasan da suka hada da Kylian Mbappe, Binicius Jr da kuma Erling Haaland su ne ‘yan wasan da suka fi tsada a duniya, a cewar wani bincike da Cibiyar Da Ke Nazari Kan Harkokin Kwallon Kafa, (CIES) Football Observatory ta gudanar.
Mbappe, mai shekara 23 a duniya, wanda ya ki amincewa ya komai Real Madrid ya gwammace ci gaba da zama a Paris St-German, shi ne kan gaba a cikin ‘yan wasa mafi tsada a duniya inda darajarsa ta kai yuro miliyan 205.6.
Dan wasan Real Madrid dan kasar Brazil Binicius Jr, wanda ya zura kwallon da ta ba su nasara a wasan karshe na gasar Zakarun Turai da suka fafata da Liverpool, shi ne na biyu mafi tsada wanda darajarsa ta kai Yuro miliyan 158.3, yayin da dan kasar Norway da ke buga wasa a Manchester City Haaland shi ne na uku inda ya kai Yuro miliyan 130.4.
Dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund Jude Bellingham (£114.1m) shi ne dan kasar Ingila mafi tsada inda yake a matsayi na biyar a wannan jadawali, inda yake gaban takwaransa na Ingila kuma dan wasan Manchester City Phil Foden, wanda yake matsayi na shida Yuro miliyan miliyan 105.9.
Kungiyoyin da ke fafatawa a Gasar Firimiya su ne suka kankame jerin ‘yan wasan da suka fi tsada inda ‘yan wasa 41 suka fito a cikin ‘yan wasan 100 da suka fi daraja kamar yadda binciken ya tabbatar.
CIES ta yi amfani da wasu muhimman abubuwa, da suka hada da shekarun dan wasa, kwazonsa da tattalin arzikin kungiyarsa da kuma hauhuawar farashi wajen gudanar da wannan bincike da ake yi.
Dan wasan Faransa Mbappe ya sanya hannu kan kwantaragin shekaru uku a kungiyarsa ta PSG a watan jiya yayin da ya zabi ci gaba da zama a kungiyar ta Paris maimakon tafiya kungiyar Real Madrid.
‘Yan wasa 10 mafi tsada a duniya
Kylian Mbappe – Paris St-Germain – Yuro miliyan 175.7. Sai kuma Binicius Jr- Real Madrid – Yuro miliyan 158.3. Erling Haaland – Borussia Dortmund kuma Yuro miliyan 130.4. Sannan Pedri – Barcelona Yuro miliyan 115.4. Akwai Jude Bellingham na Borussia Dortmund – shi kuma Yuro miliyan 114.2. Phil Foden – Manchester City – Yuro miliyan 105.9. Frenkie de Jong – Yuro miliyan Barcelona- 96.1. Luis Diaz – Liverpool – Yuro miliyan 94.0. Ruben Diaz – Manchester City – Yuro miliyan 93.6. Ferran Torres – Barcelona – Yuro miliyan 93.5.