An kama wani mutum mai suna One Mercy Orija da laifin yi wa yarinya mai shekara 12, mai suna Janet Fakeye fyade, a Abeokuta, ta jihar Ogun.
Orija, ya ce, bai dade da fito wa daga kurkukun da ke Fehintoluwa ba, a Abeokuta-taarewa da ke jihar Ogun ba.
- Xi Ya Jaddada Bukatar Inganta Farfado Da Yankunan Karkara
- NEDC Ta Raba Wa Mutanen Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa Kayan Abinci A Jihar Bauchi
Majiyarmu ta shaida mana cewa, mai laifi an taba kama shi lokaci da ya zagi wani dan sanda a bara.
Yarinyar da wannan abin ya afka wa, tana karatu ne a karamar sakandire mai suna Army Day Alamala, Abeokuta, wadda kuma shi wanda ake zargin ya ja ta da karfin tsiya zuwa wani gida wanda kuma a nan ne ake zargin ya yi mata fyaden.
Kafin Orija ya yi wa wannan yarinyar fyade, sai da ya daure hannayenta, da kafafunta ya kuma rufe bakinta, sannan ya ci gaba da yi mata fyade.
Bayan tabbatar ta faruwar wannan lamarin mahaifin yarinyar, Sanjo Fakeye, ya nemi a yi musu adalci, wajen tabbatar da hukuncin da ya dace.
“Na aiki Janet ta sayo minomo domin in wanke mata kayan makaranta. Da na ga ta dade ba ta dawo ba, sai na je gidan wata kawarta, na tambaye ta, ko ta zo wajenta, sai ta ce, ba ta ma ganta ba a wannan rana”.
“Daga nan, na tafi domin in sanar da ‘yansanda cewa, yarinyata ta bata. Tun kafin mu kai ofishin ‘yansandan, sai aka kira ni a waya, daga inda aka ga gawar ‘yata”.
“Na je na ga gawar an yi mata fyade ne har ta kai ga mutuwa”.
“An kai gawar wani sabon gida an jefar, saboda haka nake so a yi mini adalci”.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda na jihar, Abimbola Oyeyemi ya ce,’yansanda na kokarin gano inda wanda ake zargin ya gudu.
Oyeyemi ya tabbatar da cewa wanda ake zargin bai dade da fita daga kurkuku ba, ya sake aikata wannan laifin, saboda haka ya tabbatar da cewa, zai zo hannu ba da jimawa ba.