Al’ummar Kuryar Madaro da ke ƙaramar hukumar Kauran Namoda na ƙorafi game da wani sabon sansani da suka ce ‘yanbindiga sun kafa kuma su ke ci gaba da taruwa, ƙarƙashin shugabansu mai suna dan Sa’adi.
A cewarsu, wannan ɗan bindigar duk da aiyukan samar da tsaro da jami’an tsaro ke ci gaba da yi amma bai sassauta da hare-harensa ba.
“Yanzu haka wasu bakin ‘yanbindiga banda wanda muke da su, suna kafa sabbin sansanoni, wani ɗan Sa’adi ne yake jagorantarsu, kusan ya mamaye ko ina saboda yadda yake ɗaukar mutane, yana karɓar makudan kuɗaɗen.”
- Yanzu-Yanzu: Ƴan Bindiga Sun Sace Iyali 3 A Filato
- Sojoji Sun Ƙwato Makamai, Sun Ci Gaba Da Neman Bello Turji A Zamfara
Baya ga wannan ma Ɗan Sa’adi na ci gaba da tattaro ‘yan uwansa mahara, musamman waɗanda aka tarwatsa yana sake haɗa kansu, domin ci gaba da ƙaddamar da hari.
Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa har yanzu hankalinsu ba a kwance ya ke ba muddin waɗannan mahara suka ci gaba da taruwa a kusa da su.
“Mutanen nan sun matsa mana iya matsi, suna kafa sabbin sansanoni, duk wanda ke yankin nan babu wanda bai san shi ba, kuma jami’an tsaronmu na iya bakin kokarinsu.”
BBC ta tuntuɓi kakakin rundunar Fansar Yamma, Laftanar-Kanal Abubakar Abdullahi ta waya domin jin ko sun san da wannan sabon sansani, sai dai ba mu same shi ba, duk da an tura masa sakon kar-ta-kwana game da lamarin.
A kwanan nan dai rahotanni daga jihar ta Zamfara na cewa ana ci gaba da samun gagarumar nasara wajen yaƙi da ‘yan bindiga, sai ga shi yanzu wasu al’umma na bayyana cewa sabbin mahara na sake dawowa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp