Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa, ba shi da wata matsala da bai wa ƙananan hukumomi yancin gashin kan su kamar yadda kotun kolin Nijeriya ta yanke hukunci.
Sai dai gwaman ya ƙara da cewa, lallai za su sanya idanu akan duk abinda ya shafi yadda za a tafiyar da kuɗaɗen ƙananan hukumomin domin al’umma su amfana da wannan mataki.
- Matsalar Tsaro: Ɗalibai Sun Ƙaurace Wa Ɗakunan Kwana A Lakwaja
- Monguno Ya Maye Gurbin Ndume A Matsayin Mai Tsawatarwar Masu Rinjaye A Majalisa
Gwamnan ya yi wannan bayani ne a wani taro da ya kira irinsa na farko, wanda ya haɗa da ‘yan majalisar dokokin jihar Katsina da majalisar zartarwa da shuwagabannin ƙananan hukumomi da kuma ‘yan jaridu a gidan gwamnati.
A cewar gwamna Dikko Umar Raɗɗa “a matsayina na tsohon shugaban karamar hukuma, na san sha’anin gudanar da mulkin ƙananan hukumomi saboda haka, babu inda za a yi min laya.
“Wannan hukunci da kotun kolin Nijeriya ta yi, ya yi daidai da manufofin gwamnatin jihar Katsina na bai wa kananan hukumomi ‘yanci.
“Daga watan Yuni na shekarar 2023 zuwa watan Yuni na 2024, ƙananan hukumomi sun samu kuɗaɗe daga gwamnatin tarayya kimanin naira biliyan 130 da miliyan 100.” In ji Radda