Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomin Nijeriya (NULGE), ta koka kan ci gaba da jinkirin aiwatar da hukuncin da kotun koli ta yanke na bai wa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu.
Babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi ne a madadin gwamnatin tarayya; ya kai karar jihohin kasar nan 36, kan yadda gwamnonin ke tafiyar da kudaden kananan hukumomi.
- Yadda Masu Bukata Ta Musamman Suka Rungumi Sabbin Dabarun Noma Domin Ciyar Da Kansu
- NSCDC Ta Gurfanar Da Wanda Ake Zargi Da Badakalar Naira Miliyan 159
A cikin karar, mai lamba SC/CB/343/2024; babban lauyan gwamnatin tarayyar (AGF), ya kuma roki kotun da ta bayar da umarnin haramta wa gwamnonin jihohi rusa shugabannin kananan hukumomi, ba bisa ka’ida ba.
LEADERSHIP ta rawaito cewa, kukan da gwamnonin jihohi suka yi a kan kudaden kananan hukumomi ta hanyar asusun hadin gwiwa a tsakaninsu (Jihohi da kananan hukumomi), ya dakile wannan mataki na gwamnati tare da takaita ci gaban kasa a fadin kasar.
Sai dai, shekara guda cif da kotun koli ta yanke hukuncin da ya tabbatar da cikakken ikon cin gashin kai ga kananan hukumomi 774 a Nijeriya, har yanzu ba a aiwatar da shi ba a dukkanin fadin jihohin wannan kasa, kungiyar ta NULGE ta bayyana hakan a matsayin cin zarafi da gangan ga ci gaban wannan kasa.
A tattaunawarsa da da LEADERSHIP, Shugaban Kungiyar NULGE na Kasa, Aliyu Haruna Kankara, ya zargi gwamnonin jihohi da shirya wani shiri da gangan na yi wa shari’a zagon kasa, wanda hakan ke kawo cikas ga ci gaban kasa da kuma jin dadin ma’aikatan kananan hukumomi.
Kankara, ya kuma yi gargadin cewa; kungiyar za ta iya shiga yajin aiki a dukkanin fadin kasar, idan har gwamnatin tarayya ta gaza aiwatar da hukuncin da ya dace.
Kankara ya danganta jinkirin da aka samu wajen aiwatar da ‘yancin cin gashin kan, ta bangaren harkokin kudi da dabarun siyasa da gwamnatocin jihohin ke yi.
Har ila yau, ya yi zargin cewa; gwamnonin sun jajirce wajen nuna adawarsu ga ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomin tare da kawo cikas ga samun kudadensu, duk da hukuncin da kotun kolin ta yanke a 2024.
“Babu wani abu da zai hana aiwatar da wannan hukunci, sai gwamnonin da suka yi wa ‘yan Nijeriya damfara ta hanyar yin awon gaba da kudaden kananan hukumomi. Ba wata tangardar doka ba ce, illa kawai dai tsantsar adawa ta siyasa, kamar yadda shugaban ya bayyana wa LEADERSHIP.
Kotun koli ta yanke shari’a a shekarar da ta gabata tare da bayar da umarnin a biya kudaden da ake ware wa kananan hukumomi kai tsaye a cikin asusunsu, domin kauce wa katsalandan din gwamnatin jihohi. Sai dai, bayan shekara guda cif da yanke hukuncin, Kankara ya koka da yadda ba a aiwatar da hukuncin ba, musamman saboda rashin kishi daga hukumomin jihohi da na kuma tarayya.
Wannan dalili ne a cewar tasa, ya jefa kananan hukumomi cikin mawuyacin hali da kuma kunci.
Cikin takaicin jinkirin da ake yi, shugaban NULGE ya bayyana cewa; kungiyar za ta kara kaimi wajen ganin an aiwatar da hukuncin kotun kolin.
Kankara ya bayyana cewa, kungiyar za ta ci gaba da yin fafutuka tare da kulla alaka mai karfi da kungiyoyi masu zaman kansu da hukumomin kasa da kasa da kuma kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC), domin matsa wa gwamnatin tarayya lamba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp