Jam’iyyar adawa ta PDP, ta bukaci jam’iyyar APC da ta sauya akalar tsare-tsaren da suke kuntata wa al’umar kasar nan.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a game da samun ‘yancin kasa, dauke da sa hannun kakakinta, Debo Ologunagba, PDP ta ce APC ta yi wa ‘yan Nijeriya alkawura da dama wadanda ba ta cika ba.
- Gwamnatin Kaduna Ta Raba Wa Manoma Taki Buhu 120,000
- Kauyen Yugonglou Da Ya Shaida Bunkasuwar Kauyukan Kasar Sin
Daga cikin kiran da jam’iyyar adawar ta yi har da batun rage kudin man fetur da aka kara a farkon watan Satumba.
“Ya kamata ba tare da bata lokaci ba, Gwamnatin Tarayya ta rage farashin man fetur da kuma dakile faduwar darajar Naira ta hanyar sake tsara albarkatu domin farfado da sashen samar da kayayyaki da ke tangal-tangal.”
“Akwai bukatar APC ta fahimci cewa Nijeriya kasa ce mai ‘yancin kai kuma mulki yana hannun mutane.”
“Saboda haka, ya zama dole gwamnati karkashin jagorancin APC ta saurari ‘yan Nijeriya ta sake duba dukkanin manufofi da ayyukan da ba sa amfanar da jama’a wadanda ke takura rayuwa a kasar nan,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa, “hakika, ‘yan Nijeriya suna cikin radadi! dole ne a dauki mataki yanzu ta hanyar karkatar da albarkatu zuwa ayyukan da ke da tasiri kai tsaye ga jin dadin ‘yan Nijeriya.”
A baya, shugaban kasa Bola Tinubu ya sha bayyana dalilan da suka sa aka cire tallafin man fetur.
A cewar Tinubu ‘yan Nijeriya sun fi amfana da cire tallafin mai duk da cewa rahotanni na nuni da akasin hakan duba da yadda kayayyaki ke tashin gwauron zabi.
Dangane da karin kudin mai da aka yi a baya-bayan nan, Tinubu ya ce wannan hurumi ne na kamfanin mai na kasa (NNPCL), wanda ya ce ana binsa biliyoyin kudi a matsayin bashi.