Yayin taron manema labarai na yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta amsa tambayoyin manema labarai game da kalaman shugaban yankin Taiwan Lai Ching-te, tana cewa, jawabinsa, ya lalata dadaddiyar alakar dake tsakanin gabobi biyu na Zirin Taiwan, da nanata wasu kalamai kamar cin gashin kai da daukaka cikakken ’yanci, wadanda suka sake nuna taurin kan sa na neman ’yancin kan Taiwan, da bayyana aniyarsa ta ta’azzara zaman dardar a fadin Zirin Taiwan da nufin neman cimma wani muradin siyasa na kashin kai.
A cewarta, kasar Sin daya ce tak a duniya, Taiwan kuma wani bangare ne da ba zai iya ballewa ba, kuma gwamnatin Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin, ita ce gwamnati daya tilo dake wakiltar baki dayan kasar Sin. Ta kara da cewa, duk wani abu da Lai Ching-te da hukumominsa za su furta ko aiwatar, ba zai sauya gaskiyar cewa dukkan gabobin biyu na Zirin Taiwan, mallakar Sin ne ba, bare ya dakatar da daddaden burin dunkulewar kasar Sin wanda ba makawa zai tabbata. Ta ce takalar neman ’yancin kai, ba zai taba tabbatuwa ba. (Fa’iza Mustapha)