Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta kwato motoci bakwai da aka sace, sannan ta kama wasu da ake zargi da satar motocin, fashi da makami da sauran laifuka masu alaka da haka a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yansandan (PPRO), CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda yace, an kwato motocin ne bayan wasu bincike da rundunar ‘yansandan sirri (SIS) ta gudanar bisa umarnin Kwamishinan ‘yansanda, CP Ibrahim Adamu Bakori.
- Sin Na Daf Da Kaddamar Da Masana’antar Kirar Tauraron Dan’adam Mafi Girma A Asiya
- Kwankwaso Ya Tarɓi Gwamna Abba Yusuf A Abuja Bayan Kyautar NEAPS
Daga cikin motocin da aka kwato akwai Toyota RAV4 (launin toka), Peugeot 406 (ja), Toyota Corolla (baka), Toyota Yaris mai lambar Gombe 121 AH, kan babbar mota, Toyota Matrix (fara) da kuma Forland (fara) mai lamba GAK 701 XA.
“Akan haka, an kama wasu da ake zargi, ciki har da wadanda ke da hannu a fashi da makami. Wadanda ake zargin suna taimakawa wajen bincike kuma za a gurfanar da su a kotu,” in ji sanarwar.
Da yake yaba wa jami’an tsaro kan ƙwarewarsu da jajircewarsu, CP Bakori ya kuma nuna godiyarsa ga mazauna jihar kan haɗin gwiwar da suke bayar wa da kuma ci gaba da goyon bayansu ga ‘yansanda.














