Rundunar ‘yansandan Jihar Ribas ta ce ta kai samame aata maboyar ‘yan kungiyar Biyafara (IPOB) da ke karamar hukumar Oyigbo a jihar.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Okon Effiong ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin da yake gabatar da wasu da ake zargi da aikata laifukan da ke alaka da ta’addanci a sassan jihar.
- Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Da Jawabin Sabuwar Shekara Ga Majalissar CPPCC
- Tawagar Jami’an Lafiya Sinawa Ta Shirya Horo Kan Kula Da Marasa Lafiya Dake Cikin Yanayi Mai Tsanani A Sudan
A cewar Effiong, akwai ‘yan kungiyar IPOB 10 da suka hada da wadanda aka kama da hannu wajen kona ofishin ‘yansanda na Oyigbo a lokacin zanga-zangar EndSARS.
Effiong wanda ya sha alwashin cewa rundunar ba za ta kyale duk wani nau’i na miyagun ayyuka a jihar ba, ya bayyana cewa bakwai daga cikin masu garkuwa da mutane takwas da suka yi garkuwa da shugaban wani kamfanin mai a gadar sama ta Rumuokoro sun kama su tare da kubutar da wanda suka sace.
Hakan dai na zuwa ne a lokacin da jami’an rundunar suka kai farmaki kan sansanin nasu da ke Omoku.
CP Effiong, wanda ya kara da cewa, sama da mutane 120 da ake zargi da aikata laifuka an kama su da laifuka daban-daban a fadin jihar, ya fitar da kididdigar kama mutanen, wadanda aka kama da kuma wadanda suka jikkata.
“An kama mutane 22 da ake zargi da yin garkuwa da mutane 27 da ‘yan fashi da makami yayin da aka kashe jami’an ‘yansanda uku a lokacin da ake bincike,” in ji shi.
Ya kara da cewa, an kwato makamai 21 da alburusai 136, an ceto mutane 11 da aka yi garkuwa da su, sannan jami’an sun lalata wuraren hada-hadar kudi guda hudu tsakanin Oktoba da Disamba 2022.