‘Yan Sanda a jihar Binuwai da Gombe sun damke mutane 20 kan zargin garkuwa da mutane da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Kakakin Rundunar ‘yansanda ta jihar Benuwai, Catherine Anene a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata, ta ce an samu wannan nasarar ce ta hanyar hadaka da al’ummar yankin Utonkon dake Karamar hukumar Ado ta Jihar Benuwai.
Sai dai wasu mazauna yankin sun ce ‘yan bijilanti dake sintiri ne suka kama Wadanda ake zargin sannan suka mika su ga ‘yansandan.
Anene ta ce, an kuma kwato Bindiga kirar AK 47 daya da kwabsar Albarusai biyu cike da alburasai 30 masu nauyin 6.72mm.
Har ila yau , a jihar Gombe Rundunar ‘yan sanda ta jihar Gombe a jiya Litinin ta ce ta kama wani mai suna Sani Shehu dan shekara 25 da Mohammed Sani Adamu dan shekara 23 da take zargin masu garkuwa da mutane ne tare da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Kakakin Rundunar ASP Mahid Mu’azu Abubakar ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar inda ya ce dukkan su ‘yan karamar hukumar Dukku ne.
Ya ce an kama su ne a Dajin Yankari da ke jihar Bauchi a lokacin suna kan gudanar da wani taro a asirce.