Rundunar ‘yansandan Jihar Ribas, sun kama mutanen da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne 55 da ke aikata ta’asa a yankin Diobu da ke a garin Fatakwal babban birnin jihar.
An cafke su ne a wata maboyarsu da ke yankin Diobu a ranar Talata.
- Buhari Zai Halarci Nadin Sarautar Sarki Charles A Landan
- Saboda Ziyarar Tinubu, Wike Ya Ba Da Hutu, Ya Umarci Rufe Kasuwanni
Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta, ta bayyana cewa, tawagar ‘yansanda da ke yaki da ‘yan kungiyar asiri da ke caji ofis din ‘yansanda na Mile 1 ne suka kama su.
LEADERSHIP ta lura da cewa, kai samamen da kuma kamun an yi ne bayan kwanaki biyar da yin gargadin da rundunar ta yi wa ‘yan kungiyar asirin da ke aikata ta’asarsu a yankin na Diobu na bukatar da su amince da zaman lafiya su kuma tsagaita wuta kan fadan da suke yi.
Idan ba a manta ba, kimanin mutene 15 ne ‘yan kungiyar suka halaka biyo bayan wani rikici da suka yi da wata kungiyar asiri a tsakaninsu a yankin na Diobu da ke a garin na Fatakwal.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Grace Iringe-Koko ce, ta tabbatar wa da manema labarai kamun a garin Fatakwal.
Ko da ya ke, Grace ba ta fadi adadin ‘yan kungiyar asirin da aka cafke ba a lokacin samamen ba, amma ta bayyana cewa, ‘yansandan sun kai samamen ne, biyo bayan wata hatsaniya da ‘yan kungiyar asirin suka yi a yankin.