Rundunar ’Yansandan Jihar Edo, ta ceto mutane 16 da aka sace a wasu hare-hare daban-daban da aka kai a kan titunan Benin zuwa Legas da Benin zuwa Akure.
Kakakin rundunar, Joel Yamu, ya ce nasarar ta samu ne sakamakon haɗin gwiwar ’yansanda da jami’an sa-kai da mafarauta.
- Adadin Cinikayyar Sin Da Kasashen Kungiyar SCO Ya Kai Matsayin Koli A Tarihi
- Tallafin Walwalar Jama’a: Yadda Gwamnatocin Biranen Kasar Sin Ke Jifan Tsuntsu Biyu Da Dutse Daya
Ya bayyana cewa mutane shida aka ceto a kan titin Beninzuwa Akure, ɗaya daga cikinsu ya samu raunin harbin bindiga amma an taimaka masa kuma yanzu ana kula da shi a asibiti.
Haka kuma, mutane uku aka ceto a kan titin Benin zuwa Legas, sai kuma wasu mutane bakwai da aka sace a kan titin Benin zuwa Akure da aka sake su ranar 25 ga watan Agusta.
’Yansanda sun ce masu garkuwa da mutane sun tare titin a ranar 23 ga watan Agusta tsakanin ƙarfe 5:30 zuwa 6:00 na yamma, inda suka yi awon gaba da matafiya.
Bayan samum rahotom faruwar lamarin, jami’an tsaro suka bazu cikin dazuka domin ceto waɗanda suka sace.
Kwamishinan ’yansandan jihar, Monday Agbonika, ya jagoranci aikin a kan titin Benin zuwa Akure.
Ya ce sun yi amfani da sabbin fasahohi ciki har da jirage marasa matuƙa, wanda ya taimaka wajen samun nasara.
Agbonika ya yaba wa jami’an ’yansanda, sa-kai, da mafarauta bisa haɗin kai, yana mai cewa wannan haɗin gwiwa shi ne mabuɗin magance manyan laifuka.
Ya tabbatar wa jama’a cewa za su ci gaba da aiki har sai an ceto sauran mutanen da aka sace kuma an kama maharan.
“Mun ƙuduri aniyar kawar da miyagun laifuka daga titunanmu da al’ummominmu, kuma za mu yi amfani da dukkanin kayan aiki na fasaha domin kare rayukan jama’a da matafiya,” in ji kwamishinan.