Rundunar ’yansandan Jihar Katsina ta ce ta ceto mutane 28 da wasu ’yan bindiga suka sace a wasu hare-hare biyu da suka kai ƙaramar hukumar Sabuwa.
Kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce nasarar na daga cikin ƙoƙarin da Kwamishinan ’yansandan jihar, Bello Shehu, ke jagoranta domin yaƙar garkuwa da mutane da hare-haren ’yan bindiga a jihar.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 45 A Jihar Neja
- Ku Daina Kashe Mutane Ko Ku Miƙa Wuya – Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Bindiga
A ranar 29 ga watan Yuli da misalin ƙarfe 9:24 na safe, wani mutum ya kira ’yansanda tare da sanar da su cewa wasu ’yan bindiga sun tare hanyar Sabuwa zuwa Kaya, kusa da mahaɗar Inno, inda suka sace fasinjoji 14.
DPO na Sabuwa ya hanzarta tura jami’ansa zuwa wurin.
Sun fafata da ’yan bindigar inda daga bisani suka tsere zuwa cikin daji suka bar mutanen da suka sace.
An ceto dukkanin mutane 14 ba tare da wani ya ji rauni ba, amma abin baƙin ciki, wani matashi ɗan shekara 27 mai suna Abba daga garin Funtua ya rasa ransa kafin isowar ’yansanda.
A wani lamari da ya faru a ranar 28 ga watan Yuli da misalin ƙarfe 11:27 na dare, an sake kiran ’yansanda daga ƙauyen Zagaizagi, inda aka sanar da su cewa wasu ’yan bindiga sum hari tare da sace wasu mutane ƙauyen.
’Yansanda sun isa wajen suka gwabza da ’yan bindigar, kuma sun samu nasarar ceto wasu mutane 14 da kuma ƙwato shanun da aka sace guda biyu.
Amma, mutane biyu daga cikin mazauna ƙauyen sun rasa rayukansu a harin.
Rundunar ta ce har yanzu tana ci gaba da ƙoƙarin kamo ’yan bindigar da suka tsere.
Kwamishinan ’yansandan, CP Bello Shehu, ya yaba wa jami’ansa bisa jarumtaka da suka nuna.
Ya kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da bai wa ’yansanda sahihan bayanai a kan lokaci.
Ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp