Rundunar ‘yansandan jihar Katsina ta daƙile wani yunƙurin yin garkuwa da mutane a Unguwar Sarkin Fulanin Dutsen Daɗi da ke karamar hukumar Faskari tare da kuɓutar da wasu mutane 30 da ‘yan bindiga suka sace a ranar Laraba.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, DSP Abubakar Sadiq, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, inda ya bayyana hakan a matsayin gagarumar nasara a yakin da ake yi da ‘yan ta’adda a karkashin kwamishinan ‘yansandan jihar, Aliyu Musa.
- Cutar Sanƙarau Ta Kashe Mutum 26, 248 Sun Kamu A Kebbi
- Rashin Haɗin Kai Na Barazana Ga Makomar Arewa – Sarkin Zazzau
A cewar sanarwar, “Yau 12 ga Maris, 2025, da misalin karfe 01:00 na dare, hedikwatar ‘yansanda ta Faskari ta samu labari cewa, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne dauke da muggan makamai, da adadinsu mai yawa, sun kai farmaki Unguwar Sarkin Fulanin Dutsen Dadi ta kauyen Tafoki, a karamar hukumar Faskari, inda suka yi garkuwa da mutane 30, da shanu da sauran dabbobi 92.
“Bayan samun rahoton, jami’in ‘yansanda reshen Faskari ya yi gaggawar tara tawagar jami’an tsaro zuwa wurin.
“Rundunar ta hanyar amfani da dabaru, ta yi kwanton bauna, inda ta rikita ‘yan bindigar da ruwan harsashi wanda ya hakan ya ta tilasta musu guduwa da raunuka daban-daban, an yi nasarar ceto dukkan mutanen 30 da aka yi garkuwa da su ba tare da sun ji rauni ba, kuma an kwato dabbobin da suka sace.
“Kwamishanan ‘yansandan jihar Katsina, CP Aliyu Abubakar Musa, ya yaba wa jami’an da suka nuna kwazo da jajircewa wajen gudanar da aikin ceto, ya bukaci jama’ar jihar da su ci gaba da bayar da hadin kai ga rundunar ta hanyar samar da sahihin bayanai a kan lokaci domin daukar matakin gaggawa kan masu aikata muggan laifuka,” In ji Sadiq
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp