Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Kano ta fara binciken wani lamari mai ban mamaki na kisan wani Ladani mai suna Malam Zubairu, a Masallacin Yusuf Garko da ke unguwar Maraba, a yankin Hotoro.
Wannan mummunan lamari ya faru ne a ranar Litinin, 15 ga Disamba, 2025, a lokacin sallar Asuba, wanda ya bar al’ummar yankin cikin firgici.
- Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutum 3 Da Aka Sace A Kano
- Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Ta 58 A Zamfara
A cewar wani ganau, wanda ake zargin, ya isa masallacin ne da nufin yin Sallar Asuba amma Malam Zubairu ya ce masa, lokacin sallar bai yi ba tukuna.
A wani tashin hankali da ya faru ba zato ba tsammani, ana zargin matashin ya zaro wuka ya kai wa mai kula da masallacin hari, inda ya yanka maƙogwaronsa. An ruwaito cewa, wanda ake zargin ya kuma yanki wani ɓangaren maƙogwaron ya saka a cikin jaka kafin ya gudu daga wurin.
Lamarin ya hargitsa mazauna yankin, inda suka kama wanda ake zargin kuma suka kashe shi, sannan suka ƙona gidan wanda ake zargin.
Da yake tabbatar da lamarin a cikin wata sanarwa, kakakin rundunar ‘yansanda, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa, jami’an ‘yansanda sun isa wurin da wuri inda suka shawo kan lamarin.
ADVERTISEMENT














