Rundunar ‘yansandan Jihar Ogun na neman wata mata da ba a san ko wace ce ba, wadda ake zargi da jefar da wani jariri a gaban Blessed Clinic, da ke Oru Ijebu a cikin Karamar Hukumar Ijebu ta Arewa a Jihar Ogun.
- PUNCH Metro ta samu labarin cewa a ranar Asabar din da ta gabata cewa mahaifiyar ta jefar da yaron ne da misalin karfe 6:45 na safiya, a gaban asibitin, kwanaki kadan bayan ta haihu
- Matsalar ‘Yan sandan Amurka Ta Nuna Karfin Tuwo Na Kara Tsananta
- Matsalar ‘Yan sandan Amurka Ta Nuna Karfin Tuwo Na Kara Tsananta
Rundunar ta sanar da jaridar PUNCH Metro cewa mai yiwuwa yaron bai wuce kwanaki 40 ba lokacin da mahaifiyar ta yi watsi da shi.
Da ta gano jaririn a gaban asibitin, jaridar PUNCH Metro ta gano cewa, nan take mai asibitin ya shigo da yaron da aka yi watsi da shi domin samun kulawar gaggawa kafin ya tuntubi rundunar ‘yansanda ta Oru domin gabatar da rahoto.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Omolola Odutola, ya shaida wa wakilinmu cewa, an fara gudanar da bincike domin gano wadanda ke da alhakin faruwar lamarin.
Odutola ya bayyana cewa, “Likitan da ke kula da asibitin ya sanar da sashen mu game da yaron. Mun fara bincike kan lamarin, kuma a halin yanzu yaron ana jinyarsa a asibiti.”
Yin watsi da jarirai a kan tituna da wuraren zubar da ruwa ba sabon abu ba ne a Nijeriya. A shekarar 2022 ne jaridar PUNCH Metro ta ruwaito labarin wata jaririya da ba ta iya magana ko tafiya, wadda iyayenta suka yi watsi da ita a gaban wani shago dake kan titin Tajudeen Bello, titin Giwa Oke-Aro, Jihar Ogun.
Gidan marayun da aka kai ta ne suka ki amincewa da yarinyar, kuma a halin yanzu tana hannun ‘yansanda a sashen Agbado, wadanda suka ceto ta daga kan titi.
Hakazalika, a watan Janairun 2024, rundunar ‘yansandan ta cafke wata uwa ‘yar shekara 30 mai suna Olubunmi Ajayi, bisa yunkurin danna jaririnta mai watanni biyar, Imole Anifowose, a cikin kogin makarantar Sakandare ta Remo da ke yankin Sagamu a jihar.
An ce wani mutum mai suna Olusola Sonaya da ke kusa da shi ya taimaka wajen ceto jaririn bayan mahaifiyarta ta jefa ta cikin ruwa.