’Yansanda a Jihar Kogi sun gano gawar wani ɗan jarida mai ɗaukar hoto, Ayobami Aiyepeku, wanda ake zargin wani jami’in gidan gyaran hali ne ya kashe shi.
Kakakin ’yansandan Jihar Kogi, William Aya, ya ce an gano gawar a cikin daji kusa da ofishin JAMB a Lokoja, a ranar Lahadi, bayan ƙorafin da wasu mazauna yankin suka kai kan warin da ke tashi daga wajen.
- Gwamnan Kaduna Ya Sauke Kwamishinan Yaɗa Labarai, Ya Maye Gurbinsa Da Maiyaki
- Zaɓen 2027: Arewa Za Ta Sake Mara Wa Tinubu Baya — Gwamna Inuwa
Gawar wadda ta fara ruɓewa an kai ta Asibitin Ƙwararru na Jihar Kogi, yayin da ’yansanda ke ci gaba da bincike domin gano gaskiyar lamarin.
Rahotanni sun nuna cewa an kashe Ayobami ne a daren ranar Talatar da ta gabata, kuma wanda ake zargi da kisan shi ne Oluwapelumi Adebayo, wani jami’in gidan gyaran hali.
Rundunar ta ce Adebayo ya saka gawar cikin firji kafin ya jefar da ita a cikin daji.
Gwamnatin Jihar Kogi ta bayyana baƙin cikints kan kisan, inda kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Kingsley Fanwo, ya ce Gwamna Usman Ododo ya umarci hukumomin tsaro da su gudanar da bincike mai zurfi don gano gaskiyar abin da ya faru.
Ya kuma tabbatar da cewa za a hukunta duk wanda aka samu da laifi.
Iyayen marigayin Ayobami sun roƙi gwamnatin da ’yansanda da su tabbatar da an binciki lamarin yadda ya kamata kuma a hukunta waɗanda suka aikata laifin.
Yayansa, Timothy Aiyepeku, ya ce suna cikin matsanancin baƙin ciki kuma suna buƙatar sanin abin da ya faru da ɗan uwansu.
Rundunar ’yansanda ta roƙi jama’a da su bayar da duk wani bayani da zai taimaka wajen gudanar da binciken.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp