Rundunar ‘yansandan Jihar Jigawa, ta kama wasu mutane bakwai da ake zargi da hannu wajen satar shanu a jihar.
Kakakin rundunar, Lawal Shiisu ne, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Dutse ranar Laraba.
- Farashin Litar Mai Ka Iya Dawowa N900 A Bukukuwan Sabuwar Shekara – Dillalai
- Dikko Radda Ya Bai Wa Gwarazan Hikayata Kyautar Kudi
Shiisu ya ce, an kama biyu daga cikin wadanda ake zargin a ranar Talata a cikin wata mota dauke da shanu uku da tumaki 11 a yankin Ringim na jihar.
“A ranar Talata, 26/11/2024, da misalin karfe 3 na rana, rundunar ‘yansanda da sauran jami’an tsaro, a yayin da suke sintiri a kauyen Kirdau da ke Ringim, sun tare wata mota dauke da shanu uku da tumaki 11.
“Direban motar da yaronsa sun amsa cewa sun sato dabbobin ne,” in ji Shiisu.
Ya bayyana cewa, a lokacin da ake yi musu tambayoyi, sun ambaci sunayen wasu mutane biyar da suke aiki tare wadanda aka kama a unguwar Unguwa Uku da ke Jihar Kano.
“Dukkanin wadanda ake zargin su biyar sun amsa laifin aikata laifin kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike,” in ji shi.