’Yansanda a Abuja sun kama wasu shugabannin ƙungiyar masu garkuwa da mutane bayan wani samame na musamman da suka kai.
Waɗanda aka kama su ne Masud Abdullahi daga Karu, Jihar Nasarawa, wanda ake zargin shi ne shugaban ƙungiyar, da kuma Muhammad Tahir daga Jos, Jihar Filato.
- Likitoci Sun Gano Wuka Da Aka Burma A Kirjin Wani Mutum Tsawon Shekara 8
- Gwamna Dauda Zai Karɓi Baƙuncin Gwamnonin PDP A Zamfara
’Yansanda sun ce ƙungiyar ta daɗe tana addabar Abuja da kewaye da garkuwa da mutane.
Kama su ya biyo bayan wani rahoto da aka samu a ranar 16 ga wata. Agusta, 2025, cewa wasu masu garkuwa sun kai hari wata unguwa a Karu, a Abuja.
Sun shiga gidan lauya Barista Henry Chichi, inda suka yi awo gaba da shi.
Bayan kai rahoto wajen ’yansanda, rundunar yaƙi da garkuwa ta yi aiki, inda daga ƙarshe ta kuɓutar da wanda aka sace a ranar 17 ga wata Agusta da misalin ƙarfe 9:05 na dare.
A wani samame da rundunar ’yansandan Jihar Nasarawa ta kai, jami’anta sun bi sawun masu garkuwa a kan titin Nasarawa zuwa Abuja, inda motarsu Opel Vectra ja ta kife a garin Guraku.
Wasu daga cikin ’yan ƙungiyar sun tsere, amma Abdullahi da Tahir an cafke su.
Daga baya, waɗanda aka kama sun kai ’yansanda maɓoyarsu da ke dajin Karshi a Nasarawa, inda aka kama wani ɗan ƙungiyar mai shekara 22, mai suna Kabiru Jibril.
Abubuwan da aka samu a maɓoyar sun haɗa da kuɗi Naira miliyan 7.4, bindigogi AK-47 guda uku, bindiga G3 guda ɗaya, harsasai guda 16 da wayar Tecno.
Kwamishinan ’Yansandan Abuja, Ajao Adewale, ya yaba da ƙwarewa da jarumtar jami’an rundunar, tare da tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ya kuma ce suna ci gaba da bin sahun sauran ’yan ƙungiyar da suka tsere.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp