Rundunar ‘yansandan Jihar Kebbi, ta kama wasu matasa biyu da ake zargi da satar mota ƙirar Peugeot 206 a ƙaramar hukumar Shanga ranar 19 ga watan Mayu, 2025 da misalin ƙarfe 4:30 na yamma.
A cewar kakakin ‘yansandan jihar, SP Nafiu Abubakar, waɗanda aka kama su ne Umar Yusuf da Dalhatu Aminu.
- Gwamnatin Kano Ta Hana Tallace-tallacen Magungunan Gargajiya A Fina-finai Da Kan Tituna
- Hajji: Kawo Yanzu An Kammala Jigilar Maniyyatan Jihohi 12 A Nijeriya – NAHCON
An kama su ne a hanyar Shanga zuwa Dugu yayin da jami’an ‘yansanda ke binciken ababen hawa.
Motar da suke ciki ba ta da lamba, kuma suka kasa amsa tambayoyin da aka yi musu.
Sun yi yunƙurin tserewa amma aka cafke su.
Kwamishinan ‘yansandan Jihar Kebbi, CP Bello M. Sani, ya yaba da ƙoƙarin jami’ansa kuma ya umarci a miƙa lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuka (SCID) domin zurfafa bincike.
Bayan binciken, za a gurfanar da su a kotu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp