Rundunar ‘yansandan Jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane 96 da ake zargi da aikata laifuka a sassa daban-daban na jihar.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Mista Mohammed Usaini-Gumel, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Laraba a Kano.
- Buhari Ya Nemi Majalisa Ta Biya Bashin Shari’a N226bn, $556.8m, £98.5m
- LEADERSHIP Da CMG Sun Karfafa Dangantakar Aiki A Tsakaninsu
Usaini-Gumel ya ce an kama wadanda ake zargin ne da nufin samar da sauyi a jihar.
Ya ce wadanda aka kama sun hada da mutum 52 da ake zargi da laifin fashin waya da wasu miyagun kwayoyi guda shida da dillalai da kuma wasu 38 da ake zargi da satar mutane, fashi da makami, daba da kuma sata.
Kwamishinan ya ce abubuwan da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da wayoyin hannu 71, makamai 150 irin su bindigogi uku da aka kera a cikin gida, da wasu muggan makamai na kisa da dai sauransu.
Ya ce an kuma kwato kwali 20 na kodin, buhu 45 na tabar wiwi 303 daga hannun wadanda ake zargin.
Ya ce rundunar ta bullo da tsauraran matakan tsaro, domin tabbatar da kamawa da gurfanar da duk wani mutum ko gungun mutane da ke kawo cikas ga zaman lafiya a tsakanin mazauna jihar.
Ya kuma kara da cewa, “Mun kara zage damtse wajen gudanar da aikin ‘yansanda da sauran ayyukan da suka dace tare da hadin gwiwar gudanar da ayyukan leken asiri, sintiri ba dare ba rana, hada kai da sojoji da sauran jami’an tsaro ‘yan uwa,” in ji shi.
Ya kuma yaba wa al’ummar jihar bisa addu’o’i da goyon baya da kuma karfafa musu gwiwa, ya kuma yi a kira gare su da su kara kaimi kuma su kasance masu bin doka da oda da kuma kula da harkokin tsaro a kowane lokaci.
“Lambobin tuntubar mu na gaggawa su ne kamar haka: 08032419754, 08123821575 da kuma 09029292926,” in ji Usaini-Gumel.