Rundunar ‘yansandan Jihar Filato ta kama mutum 22 da ake zargi da hannu a kisan wasu ‘yan ɗaurin aure da suka fito daga Jihar Kaduna, a lokacin da suke kan hanyar zuwa biki.
Lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Yuni, 2025, a ƙauyen Mangun da ke Ƙaramar Hukumar Mangu.
- Sauye-sauyen Tinubu Suna Taimaka Wa Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya — Minista
- Buhari Ba Mutum Ne Mai Son Abun Duniya Ba – Gowon
A ranar Alhamis, 10 ga watan Yuli, 2025, rundunar ta ce za ta gurfanar da su a gaban kotu.
Baƙin da abin ya faru da su sun fito ne daga unguwar Basawa da ke Zariya, a Jihar Kaduna, kuma suna kan hanyar zuwa biki a ƙaramar hukumar Qua’an Pan da ke Jihar Filato.
Amma a garin Mangu domin tambayar hanyar da su za su, sai wasu mutane suka kai musu hari.
A harin, mutane 13 daga cikin baƙin suka rasu, ciki har da mata da yara.
Kakakin ‘yansandan jihar, DSP Alfred Alabo, ya bayyana cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargin.
Daga baya kuma, Kwamishinan ‘Yansandan zai yi jawabi a hedikwatar rundunar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp