Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ta kama mutum 4,383 tare da ceto mutane 1,138 da aka yi garkuwa da su tsakanin 31 ga watan Yuli zuwa 23 ga watan Satumba, 2025.
Sufeto Janar na ‘Yansanda, Kayode Egbetokun, ya ce cikin waɗanda aka kama akwai 481 da ake zargi da fashi da makami, 260 da satar mutane, 371 da kisan kai, 161 da mallakar bindiga ba bisa ƙa’ida ba, da kuma 322 da ake zargi da aikata fyaɗe.
- Xi Ya Bukaci Hada Karfi Da Karfe Wajen Gina Yankin Xinjiang Ya Zama Mafi Kyau
- Katsina Za Ta Ɗauki Nauyin Karatun Mahaddata Alƙur’ani – Gwamna Radda
‘Yansanda sun kuma ƙwato bindigogi 716, harsashi sama da 21,000 da motocin sata 212 a tsakanin wannan lokaci.
Egbetokun, ya bayyana cewa, jami’an rundunar sun lalata sansanonin IPOB da ESN a Kudu maso Gabas, tare da cafke wasu miyagu a jihohin Edo, Delta, Ogun, da Zamfara.
Ya ja hankalin kwamandojin ‘yansanda da su mayar da hankali wajen samar da amincewar jama’a da tabbatar da bin ƙa’ida, inda ya bayyana cewa samun goyon bayan al’umma ya fi muhimmanci sama da nuna adadin waɗanda aka kama kawai.
A cewarsa, shugabancin rundunar ya ƙuduri aniyar amfani da dabaru wajen samar da tsaro, ƙwarewar aiki, da ƙarfafa zumunci da al’umma domin rage laifuka a faɗin ƙasar nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp