Rundunar ’Yansandan Nijeriya ta kama mutane 17 da ake zargi da garkuwa da mutane tare da kashe wasu guda uku a cikin watanni biyu da suka gabata a birnin tarayya Abuja.
An kama waɗanda ake zargin ne bayan bincike mai zurfi da kuma bin diddigin ayyukansu a cikin babban birnin tarayya.
- Haɗarin Da Ke Ƙunshe Da Jin Ɓangare Ɗaya Na Labari
- NUC Da Shugabannin Makarantu Sun Yi Kira A Sanya Tsarin Kere-kere A Jami’o’in Nijeriya
Kwamishinan ’Yansandan Abuja, CP Adewale Ajao, ya bayyana cewa rundunar ta gudanar da binciken inda ta gano wuraren da ake yawan aikata laifuka, sannan aka aiwatar da tsari na musamman wanda ya kai ga nasarar kama su tsakanin watan Mayu da Yuni 2025.
Ya ƙara da cewa a cikin wannan lokaci, an samu rahoton aikata laifuka har guda 49, kuma an kama mutane 82 da ake zargi da laifuka daban-daban.
Akwai rahotannin yunƙurin garkuwa da mutane guda biyar; a Apo da Kubwa.
A yayin bincike, ’yansanda sun ƙwato motocci huɗu, wuƙa, kayan sojoji, da harsasai.
Game da fashi da makami, rahoton ya nuna cewa an samu rahotannin guda biyar daga watan Mayu zuwa Yuni, kuma an kama mutane 17 da ake zargi da aikata laifin fashin.
Kwamishinan ya kuma ce an samu rahotannin safarar yara guda huɗu, inda aka kama mutane takwas da ake zargi.
A cikin makaman da rundunar ta ƙwato akwai bindigogi AK-47 guda uku, ƙaramar bindiga ƙirar gida guda ɗaya, bindiga ƙirar Baretta, bindiga mai fitar da wuta, bindigogin LAR guda biyu, da harsasai guda 36.
Sauran abubuwan da aka kwato sun haɗa da: gatari guda ɗaya, na’urar sadarwa (walkie-talkie) guda tara, da kuɗi Naira 79,000.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp