Rundunar ’Yansandan Jihar Kano ta kama mutane 107 da ake zargi da aikata laifuka tare da ƙwato makamai masu hatsari 473 da kuma tarin miyagun ƙwayoyi.
Kwamishinan ’Yansandan Jihar, Ibrahim Adamu Bakori ne, ya bayyana haka a ranar Litinin yayin da yake bayani ga manema labarai kan nasarorin Operation Kukan Kura, wanda aka fara a watan Yuli 2025.
A cewarsa, an kama waɗanda ake zargin ne bisa laifuka irin su fashi da makami, safarar miyagun ƙwayoyi, fɗan daba, da sauran laifuka.
Ya ce aikin ya taimaka sosai wajen rage yawan laifukan daba, wanda shi ne babban matsalar tsaro a jihar.
Kwamishinan ya ƙara da cewa Operation Kukan Kura na haɗa al’umma da ’yansanda ta hanyar bayar da bayanai da goyon baya.
Ya ce wannan dabara, wadda ta yi kama da tsarin ‘community policing’, ta tabbatar da inganci wajen rage laifuka a jihar.
A cikin watan Agusta kaɗai, ’yansanda sun ƙwato fakiti 485 na ganyen tabar wiwi, kwalaye 211 na wasu kayan maye, kwalabe 257 na maganin kashe ɓeraye, da kuma ƙwayoyi 21 na Exol.
Sauran kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da wayoyi 59, POS guda uku, katin cirar kuɗi na banki 17, na’urar MP3 guda uku, tare da bindigogi, harsasai da sauran makamai masu hatsari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp